Yaƙin da ake fama da shi a Iran ya ƙara tsananta matsalar ƙarancin ruwa da ƙasar ta daɗe tana fama da ita, lamarin da masana ke cewa na iya kai tsarin samar da ruwa ga durƙushewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Tun kafin rikicin ya ɓarke, Iran na fama da matsanancin fari, yawan amfani da ruwan ƙasa fiye da kima, da kuma matsalolin tafiyar da albarkatun ruwa. Yanzu kuma yaƙin ya ƙara lalata cibiyoyin ruwa da makamashi tare da karkatar da kuɗaɗen gwamnati daga gyaran muhalli zuwa harkokin yaƙi da sake gini.
Rahotanni sun nuna cewa wasu hare-hare sun shafi cibiyoyin tace ruwan gishiri da bututun ruwa, ciki har da wata cibiyar desalination a tsibirin Qeshm da aka ce ta katse ruwa ga ƙauyuka sama da 30.
Masana sun ce matsalar wutar lantarki da lalacewar makamashi sakamakon yaƙin na hana aikin famfunan ruwa da tsarin ban ruwa yadda ya kamata, abin da ke barazana ga noma da samar da abinci.
A lokaci guda, takunkumin tattalin arziki da warewar Iran daga ƙasashen yamma sun rage damar samun sabbin fasahohin tace ruwa da hanyoyin zamani na adana ruwa.
Masana muhalli sun yi gargaɗin cewa haɗuwar yaƙi, sauyin yanayi, da matsalar tafiyar da ruwa na iya ƙara tayar da zanga-zanga da rashin zaman lafiya a cikin ƙasar, musamman a yankunan da ke fama da matsanancin ƙarancin ruwa kamar Isfahan da Khuzestan.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa yawancin madatsun ruwa a Iran sun kusa bushewa, yayin da ƙasar ke fama da ɗaya daga cikin mafi munin fari cikin shekaru da dama.
Masana sun ce idan ba a samu zaman lafiya da manyan gyare-gyare a tsarin ruwa da noma ba, matsalar ruwa a Iran za ta iya zama babbar barazana ga tattalin arziki, lafiyar jama’a, da zaman lafiyar yankin baki ɗaya.