Babachir Lawal Ya Fice Daga Jam'iyyar ADC, Ya Zargi Atiku Da Murɗiya

 Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), inda ya zargi zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyar da aka kammala kwanan nan da cewa an tafka musu gagarumar murɗiya domin fifita tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Lawal ya bayyana cewa yana barin jam'iyyar ne saboda ya amince da cewa an tafka magudi ta kowane mataki a zaɓukan fidda gwanin. Ya yi zargin cewa tun kafin a yi zaɓen aka riga aka tsara sakamakon da gangan domin ya yi daidai da muradin sansanin Atiku.

Haka kuma, ya yi ikirarin cewa an sauya tsare-tsaren cikin gida na jam'iyyar, inda a wasu lokutan ma aka soke sakamakon gaskiya domin ɗora ƴan takarar da ake so.

Tsohon Sakataren ya bayyana halin da jam'iyyar ke ciki a matsayin abin damuwa ƙwarai da gaske, yana mai cewa ba zai iya ci gaba da zama a cikin mahallin da yake amincewa da zaluncin siyasa ba.

A cewarsa, ci gaba da zama a ADC zai mayar da shi wani ɓangare na tsarin da zai iya amfani da irin waɗannan dabarun magudi yayin da ake fuskantar babban zaɓen shekarar 2027.

Haka zalika, Lawal ya bayyana cewa lamirinsa da imanin da yake da shi a siyasance ba su dace da alkiblar da jam'iyyar ta kama ba a yanzu. Ya jaddada cewa ya shiga jam'iyyar ADC ne da fatan bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa, ba wai don ya zama ɓangare na lalataccen tsari da durƙushewar tsarin dimokiraɗiyyar cikin gida ba.

Tsohon SGF ɗin ya ƙara da cewa yanzu zai sake duba alkiblarsa ta fuskar siyasa, kuma zai tattauna da mutanen da suke da ra'ayi ɗaya da shi kan hanyar da za a bi nan gaba.

Ya bayyana cewa a halin yanzu zai mayar da hankali ne ga harkokinsa na kashin kansa, da suka haɗa da aikin gona a mahaifarsa, yayin da zai ci gaba da lura da yadda al'amuran siyasa ke sauyawa gabanin babban zaɓe mai zuwa.

Wani ɓangare na sanarwar tasa na cewa:

"Ina fita daga ADC ne saboda zaɓukan fidda gwanin da aka kammala an tafka musu gagarumin magudi ta kowane mataki domin fifita Kachalla Abubakar Atiku. Ina hango wata makarkashiya ta yin gum da baki wadda ba na son zama ɓangarenta. Yawancin mambobin jam'iyyar suna nuna hali kamar abin da aka yi shi ne daidai.

"Kawai rubuta sakamakon aka yi ko aka sake rubuta shi don amfaninsa da kuma na gungunsa. Sannan ko a wuraren da aka ɗan ba da damar yin tamkar zaɓe, kawai sai aka maye gurbin waɗanda suka yi nasara da mambobin ƙungiyarsa. A taƙaice dai, abin da aka yi wasan kwaikwayo ne na abin kunya.

"Ina yin hakan ne saboda ba na da niyyar zama ɓangare na na'urar magudin zaɓe ta Kachalla Atiku a babban zaɓen 2027, kuma ba zan iya kauce wa hakan ba idan na ci gaba da zama a jam'iyyar. Shi da gungunsa tsirarun mutane ne masu ra'ayin kabilanci na Fulani da kuma masu son kafa mulkin kama-karya na addini.

"A gare ni, yi wa Kachalla Atiku aiki yana nufin ba wa Tinubu tikitin atomatik na zarcewa wa'adi na biyu, wanda wannan abu yana ba ni tsoro ƙwarai da gaske. Na yi amanna cewa idan aka kwatanta, Tinubu zai iya zama shugaban ƙasa mafi alheri ga Nijeriya fiye da yadda Kachalla Atiku zai taɓa kasancewa (duk da irin murnar da Tinubu yake da ita a yanzu da kuma yadda zai iya kasancewa a nan gaba)."

Post a Comment

Previous Post Next Post