Gwamnatin Tarayya Za Ta Ci Gaba da Tallafa wa Ƙananan Kasuwanci — Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta ci gaba da samar da ingantaccen yanayi da zai ba ƙananan, matsakaita da manyan ƙananan masana'antu (MSMEs) damar bunƙasa, yana mai cewa waɗannan kasuwanci su ne ginshiƙin tattalin arzikin Najeriya.Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja yayin bikin karrama fitattun MSMEs karo na takwas na ƙasa (8th National MSME Awards), inda ya ce gwamnati na gina cikakken tsarin da ke ƙarfafa kirkire-kirkire, samar da muhimman ababen more rayuwa da kuma kawar da matsalolin da suka dade suna hana ƙananan kasuwanci ci gaba.

Mataimakin Shugaban Ƙasar, wanda Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, ya wakilta, ya buƙaci waɗanda suka lashe kyaututtukan da sauran 'yan kasuwa su ci gaba da ƙoƙarin bunƙasa sana'o'insu, yana mai tabbatar musu da cikakken goyon bayan gwamnati.

Ya ce, "Najeriya na buƙatar sabbin dabarunku, ayyukan yi da kuke samarwa da kuma jagorancinku. Ina da tabbacin cewa gwamnatin tarayya tare da gwamnatocin jihohi da abokan hulɗarmu a ɓangaren masu zaman kansu za su ci gaba da gina ƙasar da kasuwanci ke jagoranta, inda ake ba kirkire-kirkire lada, ƙananan kasuwanci su zama manyan kamfanoni, kuma arziki ya amfanar da kowa."

Shettima ya bayyana cewa kusan kashi 90 cikin 100 na dukkan kasuwancin Najeriya MSMEs ne, kuma su ne mafi girman masu samar da ayyukan yi a ƙasar, inda suke ɗaukar sama da mutum miliyan 60 aiki.

Ya ce ta hanyar jajircewa, kirkire-kirkire da himma, waɗannan kamfanoni na inganta rayuwar 'yan Najeriya tare da kawo ci gaba a al'ummomi.

A cewarsa, saboda muhimmancin MSMEs ga tattalin arzikin ƙasa, ɗaya daga cikin manyan manufofin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu shi ne samar da yanayin da zai ba su damar bunƙasa, maimakon dogaro da tallafi ko rance kawai.

Shettima ya bayyana cewa tun daga shekarar 2023, gwamnatin tarayya ta faɗaɗa shirin National MSME Clinics tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi, inda aka kai shirin zuwa dukkan shiyyoyin siyasa shida na ƙasar.

Ya ce wannan shiri ya bai wa masu ƙananan kasuwanci damar tattaunawa kai tsaye da hukumomin gwamnati, cibiyoyin kuɗi da ƙungiyoyin tallafa wa kasuwanci domin samun mafita cikin gaggawa ga matsalolinsu.

Ya kuma ce gwamnati ta kafa cibiyoyi 21 na zamani masu kayayyakin aiki da ake amfani da su tare (Shared Infrastructure Facilities), waɗanda ke samar da intanet mai sauri, injuna na zamani da wuraren aiki na haɗin gwiwa ga masu fasahar zamani da masu sana'o'i, lamarin da ya taimaka wajen samar da ayyukan yi sama da 650,000.

Game da tallafin kuɗi, Shettima ya ce gwamnati ta ƙaddamar da Asusun Tallafawa MSMEs na naira biliyan 75 da kuma Shirin Tallafin Shugaban Ƙasa na naira biliyan 50, domin ƙara wa ƙananan kasuwanci damar samun jari.

Ya ƙara da cewa ta hannun Development Bank of Nigeria (DBN) an raba naira biliyan 874 ga kusan MSMEs 751,000 da mata da matasa ke jagoranta.

Hakazalika, ya ce Nigerian Export-Import Bank (NEXIM) ta samar da tallafin kuɗi da ya kai naira biliyan 394.88 ga kamfanonin da ke fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

Ya kuma bayyana cewa a ƙarƙashin shirin Skill-Up Artisans, gwamnati ta horar da sama da masu sana'a 165,000 tare da samar musu da kayan aikin da za su taimaka musu wajen bunƙasa sana'o'insu.

Dangane da littafin da aka ƙaddamar a wajen taron mai taken "Building Nigeria, Empowering MSMEs: A Compendium of the Federal Government's Initiatives and Interventions for Nigerian MSME Growth," Shettima ya ce littafin ya tattara dukkan manyan shirye-shiryen gwamnati na tallafa wa MSMEs, kuma yana nuna jajircewar Shugaba Tinubu wajen bunƙasa kasuwancin Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa bikin MSME Awards wani muhimmin ɓangare ne na aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda, yana mai cewa tun bayan fara bayar da kyaututtukan, fiye da ƙananan 'yan kasuwa 50 aka karrama saboda gudummawar da suka bayar ga tattalin arzikin ƙasa.

A cewarsa, a wannan karo na takwas, gwamnati ta sauya tsarin kyaututtuka, inda maimakon bayar da motoci, gidaje ko shaguna kamar yadda aka saba a baya, ta fi mayar da hankali kan bayar da kuɗaɗen jari domin taimaka wa kasuwancin da suka ci nasara su bunƙasa.

A nasa jawabin, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Samar da Ayyukan Yi da MSMEs, Mista Temitola Adekunle-Johnson, ya ce bikin na shekarar 2026 ya bai wa masu buƙata ta musamman da kuma fitattun kamfanoni masu kirkire-kirkire damar samun karramawa.

Shi ma Darakta Janar na Standard Organisation of Nigeria (SON), Dakta Ifeanyi Okeke, wanda Misis Phebian Arumemi ta wakilta, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen waɗanda suka yi nasara cikin tsauri bayan an karɓi buƙatu 13,859 daga sassan ƙasar.

Ya ce an zaɓi waɗanda suka yi nasara daga fannoni daban-daban da suka haɗa da noma, fasahar sadarwa, masana'antun kirkire-kirkire, aikin katako, sana'ar fata, kayan kwalliya, masana'antu, salo da kuma masu buƙata ta musamman.

An kuma ƙaddamar da littafin "Building Nigeria, Empowering MSMEs", wanda Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Samar da Ayyukan Yi da MSMEs, Mista Temitola Johnson ya rubuta, yayin da Babban Mataimaki na Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Mista Stanley Nkwocha, ya gabatar da shi.

Daga cikin waɗanda suka lashe kyaututtukan MSME na shekarar 2026 akwai Olanreforward Foods & Farms Ltd, wadda ta lashe kyautar MSME of the Year, tare da samun lambar yabo kan bin ka'idojin biyan haraji. Sauran waɗanda suka yi nasara sun haɗa da Myria Gee Ltd, DX Inception Ltd, Fary Business Trade and Supply Company Ltd, Aljamus Technologies and Consulting Services Ltd, Ennie Wears Ltd, Skarabrand Furniture & Decor Solutions, Lylocee Designs & Fashion World, Vivido Schone Int'L Ltd, Mdu Ecochange Solution Ltd, Kosai Republic da Arlecode (Acana Makeover), waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na kasuwanci da kirkire-kirkire.

Post a Comment

Previous Post Next Post