Isra'ila tana ganin idan kasar Iraki ta mallaki makaman nukiliya to kashinta ya bushe. Operation Opera": Harin Jiragen Isra'ila ne a kan tashar makaman Nukiliya na Iraki. Isra'ilawa sun girgiza duniya da gaggarumin harin jiragen F-16 na farko.
A Ranar Lahadi, 7 ga Yuni, 1981. Isra'ila ta kai hari Cibiyar Binciken Nukiliya ta Al-Tuwaythah, dake wajen birnin Baghdad, Iraq. Operation Opera wanda aka fi sani da Operation Babylon, wani harin ba-zata ne da sojojin saman Isra'ila suka kai a ranar 7 ga watan Yunin 1981, wanda ya lalata wasu makaman nukiliyar Iraqi da ba a kammala ba.
Harin Isra'ila ya zo ne shekara guda bayan da sojojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka yi mummunar barna a kan makaman nukiliyar Iraki a cikin Operation Scorch Sword, Iraki ta gyara barnar da aka yi daga bisani ta hanyar hada guiwa da kasar Faransa.
Operation Opera, da kuma bayanan gwamnatin Isra'ila da suka biyo bayansa, sun kafa dalilin cewa basa so wata kasa a yankin Gabas ta tsakiya ta mallaki makamin nukiliya domin zai zama barazana ga tsaron ta.
Tun a shekarar 1976 kasar Faransa ta fara taimakawa kasar Iraki a karkashin jagorancin Saddam Hussein don kokarin hada makamantan na nukiliya.
A cikin 1976, Iraki ta kulla yarjejeniya da Faransa wanda ya yi wa Iraki alkawarin samar mata da Nukiliya guda biyu wanda aka yiwa lakabin Tamuz na 1 da Tamuz 2. Wannan ya kasance barazana ga Isra'ila kuma a bayyane yake cewa dole ne Isra'ila ta kawar da wadannan makaman nukiliyar, a cewar kasar.
Jiragen Isra'ila sun tashi daga filin jiragen saman Etizion na Isra'ila, ba tare da wata sanarwar rediyo ba, sunyi tafiyar 1100km, sun je sun ruguza tashar nukiliyar Osirak ta Iraki, kowane jirgin saman yaki ya jefa bama-bamai.
An ayyana Operation Opera a matsayin wanda yayi nasara kuma dukkan matukan jirgin sun koma Isra’ila lafiya. Wannan farmakin ya taimaka wajen hana gwamnatin Iraki samun makamin kare dangi.
Jami'in diflomasiyyar Isra'ila Yehuda Zvi Blum, a wani jawabi da ta yi wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bayan harin, ya yi ikirarin cewa an kaddamar da aikin ne a ranar Lahadi da yamma bisa tunanin cewa ma'aikatan da ke wurin, ciki har da kwararru yan kasashen waje da ke aiki a ma'aikatar, sun tashi, a lokacin, amma duk da wannan taka tsantsan, akwai ɗaruruwan ma'aikatan Faransawa da wasu 'yan ƙasar Iraki a masana'antar a lokacin harin.
Sojojin Iraqi goma da farar hula 1 ne aka kashe a harin. Farar hula da aka kashe shi ne dan kasar Faransa injiniya Damien Chaussepied mai shekaru 25, wanda ma'aikaci ne na Air Liquide da hukumar gwamnatin Faransa CEA. A cikin 1981, Isra'ila ta amince ta biya diyya ga dangin Chaussepied.
