Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta sanar da rufe mashigar Hormuz ga dukkan jiragen ruwa, tare da gargadin cewa kada su kusanci yankin.
Ta zargi Amurka da Isra’ila da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, abin da ya kara dagula yanayin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙaruwar tashin hankali a yankin, musamman bayan zargin ci gaba da kai hare-hare duk da yarjejeniyar dakatar da faɗa.
Rundunar ta ce matakin da ta dauka ya biyo bayan abin da ta kira saɓawa yarjejeniyar da aka kulla domin kawo karshen rikici.
IRGC ta nuna damuwa kan hare-haren da ake zargin Isra’ila na kai wa a kudancin Lebanon, tana mai cewa hakan na daga cikin manyan dalilan da suka sa aka rufe mashigin.
Ta ce wannan na nuna rashin cika alkawuran da aka dauka a yarjejeniyar tsagaita wuta.
A wani bangare, rundunar ta fitar da kakkausar gargadi ga dukkan jiragen ruwa, tana mai cewa duk wanda ya kuskura ya kusanci mashigar zai iya jefa kansa cikin hadari.