An yi Musayar Yawu Tsakanin Furaministan Italiya da Donald Trump

Musayar yawu tsakanin Shugaba Trump da firaministar Italiya, Giorgia Meloni ta ci gaba da faɗaɗa, bayan da shugaban Amurka ya jaddada iƙirarinsa cewa Ms Meloni ta roƙe shi su ɗauki hoto tare a taron ƙungiyar ƙasashe masu arziki ta G7 da aka gudanar a baya-bayan nan. Wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya yi iƙirarin cewa shugabar Italiya ''ba ta yi daidai da matakin shahararta ba''.

A nata ɓangare Ms Meloni ta mayar da martani, cikin wani saƙo da ta wallafa tana mai cewa shahararta ba damuwar Trump ba ne - don haka ya mayar da hankali ga tasa shaharar.

A baya dai shugabannin biyu masu tsattsauran ra'ayi sun kasance manyan abokai, to sai dai dangantar tasu ta yi tsami bayan da aka bayar da rahoton cewa Italiya ta hana sojojin Amurka damar amfani da sansaninta da ke Sicily don kai hare-hare zuwa cikin Iran.

Post a Comment

Previous Post Next Post