Iran Ta Sake Kai Harin Ramuwar Gayya

Iran Ta Kai Hari Kan Sansanin Sojin Amurka da Hedikwatar Fifth Fleet a Matsayin Ramuwar Gayya

Rundunar juyin juya halin ƙasar Iran (IRGC) ta ce dakarunta sun kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙi kan sansanin sojin Amurka da kuma hedikwatar rundunar sojin ruwa ta Fifth Fleet.

Iran

A cikin sanarwar da ta fitar, IRGC ta ce matakin ya biyo bayan abin da ta kira harin da Amurka ta kai kan wani tankar mai na Iran kusa da mashigin Hormuz, wanda ya jawo lalacewar sashen injin jirgin.

Ta kuma ce bayan wani hari da Amurka ta kai kan wata tashar sadarwa a tsibirin Qeshm, dakarunta na sama sun kai farmaki kan sansanin sojin Amurka da ke wani ƙasa a yankin, da kuma cibiyar umarnin Fifth Fleet.

Sanarwar ta yi gargadi cewa duk wani abin da zai kawo barazana ga tsaro a mashigin Hormuz zai fuskanci martani mai tsauri daga Iran.

Post a Comment

Previous Post Next Post