Isra’ila Da Iran Sun Ci Gaba da Musayar Hare-Hare Yayin Da Tsagaita Wuta Ke Kara Lalacewa

 Israel da Iran sun ci gaba da musayar hare-haren sama da makamai masu linzami yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin ke nuna alamun rushewa.

Israel da Iran

Rahotanni sun ce Iran ta harba makamai masu linzami zuwa wasu yankuna a Isra’ila bayan hare-haren da Isra’ila ta kai a Lebanon da wasu wurare da ake dangantawa da ƙawayen Tehran. A martani, Isra’ila ta kai sabbin hare-hare kan wuraren soja da cibiyoyi a cikin Iran. 

Jami’an tsaro sun bayyana cewa tsarin kariyar sararin samaniya ya kakkabo wasu daga cikin makaman da aka harba, yayin da aka ji ƙarar fashe-fashe a birane daban-daban a ƙasashen biyu. 

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga ɓangarorin da su kwantar da hankali tare da komawa tattaunawa, amma rikicin ya ci gaba duk da ƙoƙarin diflomasiyya. 

Masana siyasa sun ce ci gaba da hare-haren na iya ƙara dagula rikicin Gabas ta Tsakiya tare da jefa yarjejeniyar tsagaita wuta cikin haɗari mai tsanani. Haka kuma ana fargabar rikicin zai iya shafar farashin mai da tsaron hanyoyin jiragen ruwa a yankin Gulf. 

Ƙungiyoyin duniya da United Nations sun sake yin kira da a dakatar da tashin hankalin domin hana rikicin ya koma babban yaƙi a yankin. 

Post a Comment

Previous Post Next Post