Hukumomi a sassa daban-daban na Jamus na ci gaba da kokarin shawo kan wata mummunar barkewar annobar wasu kwari masu guba da ake kira oak processionary moth caterpillars, wadanda ke haddasa matsalolin lafiya masu tsanani tare da tilasta rufe wuraren shakatawa da sauran wuraren bude ido, ciki har da a babban birnin ƙasar, Berlin.
Waɗannan ƙwari na da ƙananan gashin da ba a iya gani da ido cikin sauƙi, masu ɗauke da wata guba da kan haddasa kuraje a fata, kumburin ido (conjunctivitis) da kuma matsalolin numfashi idan suka taɓa jikin mutum. Gashin na da sauƙin watsewa kuma iska na iya ɗaukar su zuwa nesa, lamarin da ke ƙara haɗarin kamuwa da illarsu.
Baya ga haka, ƙwarin na gina fararen gidaje masu kama da zaren siliki a jikin bishiyoyin oak da suka mamaye. Waɗannan gidajen ma suna ɗauke da dimbin gashin gubar da ke ƙara barazana ga lafiyar jama'a.
Matsalar ta fi kamari a birnin Berlin, musamman a gundumomin Charlottenburg-Wilmersdorf, Spandau da Friedrichshain-Kreuzberg, waɗanda hukumomi suka bayyana a matsayin wuraren da barkewar ta fi tsanani.
Sakamakon haka, da dama daga cikin fitattun wuraren shakatawa na birnin sun koma tamkar wuraren da aka killace saboda aikata laifi, inda aka sanya jan da farin igiyoyin gargadi domin hana mutane kusantar wuraren.
A gundumar Spandau da ke yammacin Berlin, hukumomi sun bukaci jama'a su guji ziyartar filin shakatawa na Wilhelm-von-Siemens-Park mai fadin eka 39, tare da makarantu, cibiyoyin kula da yara da kuma titunan da ke kusa da wurin.
A ziyarar da tashar CNN ta kai filin shakatawa na Jungfernheide, wanda shi ne na biyu mafi girma a Berlin kuma ɗaya daga cikin wuraren da suka fi fama da barkewar, an ga ma'aikata bakwai sanye da cikakkun kayan kariya masu launin shuɗi da abin rufe fuska na musamman, suna amfani da manyan injinan tsotsa irin waɗanda ake amfani da su wajen cire sinadarin asbestos domin shanye gidajen ƙwarin daga rassan bishiyoyi masu tsayin kusan mita 20.
Hukumomi sun bayyana cewa amfani da irin waɗannan injuna na tabbatar da cewa babu ko ɗaya daga cikin kusan ƙananan gashin guba 700,000 da kowanne ƙwari ke ɗauke da su da ke tserewa zuwa iska.
Wani jami'in birnin da ke kula da aikin ya shaida wa CNN cewa bishiyoyi kusan 2,000 a cikin filin shakatawar sun kamu da wannan matsala, kuma an killace yankunan da suke. Ya amince cewa babu wata hanya ta kawar da matsalar gaba ɗaya, yana mai cewa abin da ake yi yanzu shi ne rage haɗarin da take haifarwa ta hanyar fara tsaftace bishiyoyin da ke kusa da hanyoyin da baƙi ke bi.
Jami'in ya ƙara da cewa burinsu shi ne su tsaftace bishiyoyi kusan 20 a kowace rana, sai dai yawan gidajen ƙwarin na bambanta daga bishiya zuwa bishiya. A cewarsa, a ƙarshen makon da ya gabata, wata ƙungiyar ma'aikata ta shafe yini guda tana cire gidaje kusan 800 daga bishiya guda ɗaya.
Rahotanni sun kuma nuna cewa an samu irin wannan barkewar a birnin Hamburg da kuma jihar North Rhine-Westphalia da ke yammacin Jamus. Bayanai daga shafin EPS-Radar, wanda ke bibiyar wuraren da barkewar ke faruwa ta hanyar taswirar dijital, sun tabbatar da yawaitar matsalar.
Mai ƙirƙirar shafin, Britta Wunderwald, ta bayyana wa CNN cewa duk da aikinta na kasuwanci da tallace-tallace, ta ƙirƙiri taswirar ne tare da taimakon wata fasahar basirar wucin gadi (AI), bayan ɗan wani abokinta ya nuna alamomin da suka dace da waɗanda ke bayyana bayan mutum ya taɓa waɗannan ƙwari masu guba.
Ta ce ta fara tunanin ko za ta iya fita waje lafiya ko kuma inda za ta samu wurin yin fikinik ba tare da haɗari ba, amma ta gano cewa babu wata taswira da ke nuna wuraren da barkewar ta shafa a bana.
Wunderwald ta bayyana fatan cewa daga shekara mai zuwa hukumomin ƙananan hukumomi za su ɗauki matakan kariya tun kafin barkewar ta tsananta, domin kare lafiyar jama'a.