LEGAS, NAJERIYA — Wani ginin shaguna mai hawa uku ya rushe a yankin Alakija da ke Jihar Legas a ranar Alhamis, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda, yayin da aka ceto wasu mutane 10, sannan ake fargabar adadin mutanen da ba a tantance ba sun makale a karkashin barbashin ginin.
Ginin, wanda ke kan titin 'Old Ojo Road' kusa da tashar mota ta Alakija, daidai hanyar Legas zuwa Badagry a garin Satellite Town, ya rushe ne da misalin karfe 11:40 na safe. Wannan lamari ya sanya Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) da sauran hukumomin ceto gaggawa mamaye gurin da gudu domin gudanar da aikin ceto.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, Babban Sakataren LASEMA, Dr. Olufemi Oke-Osanyintolu, ya bayyana cewa ana tsaka da gudanar da hadin gwiwar aikin ceto domin zakulo tare da fito da wadanda suka makale a karkashin barbashin ginin.
"Hukumar LASEMA ta kaddamar da shirin tallafin gaggawa biyar bayan rushewar ginin shaguna mai hawa uku a Alakija, da ke karkashin Hukumar Raya Karkara ta Ori-Ade (LCDA)," in ji shi.
A cewarsa, jami'an ceto suna gudanar da bincike na tsanaki a gurin, yayin da fargaba ke karuwa kan cewa wasu karin mutanen na iya kasancewa a makale har yanzu.
"A halin yanzu ana tsaka da gudanar da aikin ceto na hadin gwiwa tsakanin hukumomi daban-daban, inda jami'an ceto ke aiki daki-daki domin neman da kuma fito da duk wani da ke makale a karkashin barbashin ginin," in ji Oke-Osanyintolu.
Ya bayyana cewa an ceto mutane biyu da rayukansu da fari, yayin da aka gano gawar mutum guda. Daga baya, adadin wadanda aka ceto ya karu zuwa mutum 10 sakamakon ci gaba da aikin ceto.
"An ceto mutane da rayukansu ta hanyar hadin gwiwar hukumomin LASEMA, LASBCA, da kuma Kamfanin Ginin Hanya na CRCC. Haka kuma an gano gawar wani babban namiji guda daya. Ana nan ana ci gaba da kokarin fito da sauran," in ji shi.
Shugaban na LASEMA ya kara da cewa, rahotanni daga gurin da lamarin ya faru sun nuna cewa sauran mutane, da suka hada da masu shaguna wadanda suka riga suka bude kasuwancinsu na ranar, na iya kasancewa a makale a cikin ginin da ya rushe.
"Akwai rahotannin da ke nuna cewa karin wasu mutane, da suka hada da masu shagunan da suka dawo bakin ayyukansu, na iya kasancewa a makale. Ayyukan bincike da ceto suna nan suna gudana gadan-gadan," in ji shi.
Haka kuma ya bayyana cewa an tura manyan kayan aiki na zamani domin taimakawa wajen aikin ceton.
"An tura manyan injina, ciki har da injin tono kasa da kwashe bargaza (excavator), domin tallafawa kokarin ceto mutanen," in ji Oke-Osanyintolu.
Daga karshe, ya yi kira ga mazauna yankin da su nesanta kansu da gurin da lamarin ya faru domin bai wa ma'aikatan agaji damar gudanar da ayyukansu cikin sauki ba tare da tsangwama ba.
"Muna shawartar mambobin jam'ar gari da su kwantar da hankulansu, su guji zuwa gurin da abun ya faru, sannan su bai wa jami'an agajin gaggawa cikakkiyar hanya domin gudanar da ayyukan ceto rayuka," in ji shi.