OSOGBO, NAJERIYA — Tsohon dan.
Oyintiloye ya yi wannan kiran ne yayin da yake taya 'yan Najeriya murna bisa amincewar da Majalisar Dattawa (Sanat) ta yi wa batun kafa 'yan sandan jihohi. Ya bayyana wannan ci gaba a matsayin wani muhimmin mataki na tarihi a kokarin da kasar ke yi na samar da tsarin tsaro mai inganci, cikin sauri, da kuma wanda ya ginu a kan al'umma.A cikin wata sanarwa da aka rarraba a garin Osogbo a ranar Alhamis, jigo a jam'iyyar APC ya bayyana cewa tsaro ya fi yin tasiri ne idan ya kasance daga cikin gida yake fitowa, kuma aka gina shi bisa bayanan sirri tare da goyon bayan al'umma.
"Shekaru da yawa na kasance mai fafutuka da babbar murya wajen ganin an kafa 'yan sandan jihohi, domin na yi amanna cewa yanayin tsaron Najeriya na yanzu yana bukatar tsarin tsaro na cikin gida. A yau, ina farin cikin cewa wannan dogon buri na kasarmu ya zama gaskiya a karkashin jajirtaccen shugabanci mai hangen nesa na Shugaban Kasa," in ji shi.
Yayin da yake bayyana amincewa da tsarin 'yan sandan jihohi a matsayin mataki da ya dace, Oyintiloye ya bayyana cewa kasar tana bukatar amfani da tsarin tsaro mai matakai daban-daban domin fuskantar sabbin matsalolin tsaro da ke kunno kai.
"Gaskiyar magana ita ce, Najeriya tana bukatar karin wasu hukumomin 'yan sanda. Abu ne mai kyau da yanzu muke da 'yan sandan jihohi, kuma mataki ne da ya dace. Amma bayan haka, ya kamata mu sami wasu tsare-tsaren na 'yan sanda. Ya kamata mu sami 'yan sandan manyan hanyoyi (Highway Police), 'yan sandan yawon bude ido (Tourist Police), da sauran su," in ji shi.
Tsohon dan majalisar ya nuna gamsuwarsa da yadda fafutukar da ya dade yana yi ta samu karbuwa a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya tunatar da cewa ya dade yana bayyana ra'ayinsa cewa kafa 'yan sandan jihohi shi ne mafita ta gari ga matsalolin tsaron Najeriya. Ya buga misali da wata kasidarsa da aka wallafa a wata jaridar kasa a ranar 25 ga Fabrairu, 2018, inda a lokacin ya bukaci da a rarraba ikon rundunar 'yan sanda domin magance matsalolin tsaro na musamman da suka shafi kowane yanki na kasar.