Kalaman Ministan Tsaron Nijeriya Na Ci Gaba Da Tada Kura A Fadin Kasar

"Allah ne Kaɗai Zai Iya Kawo Ƙarshen matsalar Rashin Tsaro a Najeriya” in ji ministan Tsaro Matawalle.

Bello Matawalle

Karamin Ministan Tsaro na Ƙasa mai kula da Harkokin Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa Allah kaɗai ne zai iya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana addabar Najeriya.

Matawalle ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnati da jami’an tsaro ke yi wajen yaƙi da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran ayyukan miyagu, babu wani ɗan Adam da zai iya cewa zai kawar da matsalar gaba ɗaya sai da ikon Allah. 

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da ɗaukar matakai da ƙarfafa rundunonin tsaro domin magance matsalar. 

Kalaman ministan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan hanyoyin da za a bi wajen kawo ƙarshen hare-haren ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar. 

Matawalle ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai tare da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post