Kotun Tunisia Ta Yanke Wa Shugaban Ennahdha, Rached Ghannouchi, Hukuncin Daurin Rai da Rai

 Wata kotu a ƙasar Tunisia ta yanke wa jagoran jam’iyyar adawa ta Ennahdha, Rached Ghannouchi, hukuncin daurin rai da rai bisa zarge-zargen da suka shafi ta’addanci da kuma kafa wata “ƙungiyar sirri” ta tsaro. 

Rached Ghannouchi

Kotun da ke sauraron shari’o’in ta’addanci a birnin Tunis ta yanke hukuncin ne tare da wasu mutane sama da 30 da ake zargi da hannu a abin da hukumomi suka kira “secret apparatus” na jam’iyyar Ennahdha. 

Rahotanni sun ce Rached Ghannouchi, wanda tsohon kakakin majalisar dokokin Tunisia ne, ya samu hukuncin ɗaurin rai da rai tare da ƙarin shekaru 30 a gidan yari. 

An kuma yanke wa mataimakinsa, Ali Larayedh, hukuncin shekaru 42 a gidan yari, yayin da wasu tsoffin jami’an tsaro da mambobin jam’iyyar suka samu hukuncin shekaru tsakanin 10 zuwa rai da rai. 

An buɗe shari’ar ne bayan koke da aka shigar tun shekarar 2022 dangane da zargin cewa jam’iyyar Ennahdha ta kafa wata cibiyar tsaro ta ɓoye da ake dangantawa da kashe ‘yan siyasa biyu a shekarar 2013.

Sai dai jam’iyyar Ennahdha ta musanta dukkan zarge-zargen, tana mai cewa ana amfani da kotuna ne domin murƙushe ‘yan adawa da masu sukar gwamnatin shugaban ƙasa Kais Saied. 

Rached Ghannouchi na tsare tun watan Afrilun 2023, kuma ya riga ya fuskanci wasu hukuncin kurkuku daban-daban a shekarun baya kan zarge-zargen da suka haɗa da cin hanci, tallafin waje ba bisa ƙa’ida ba, da kuma ta’addanci. 

Post a Comment

Previous Post Next Post