Kungiyoyi Marasa Uba (‘Ya’yan Shegu)

Ba matsala ba ne don ka kira Ahlus Sunna da sunan "Wahabiyya", saboda laƙabi ne da yake kamar "Malikiyya" da sauransu.

Kuma wannan "Wahabiyancin" ya girmi ƙungiyarka. Manyan Malamansa sun girmi shehunanku.

Shaikh Muhammad bn AbdilWahhab ya girmi Shehu Tijjaniy, wanda ya kawo wannan bala'i na Tijjaniyanci cikin al'ummar Musulmi. Balle kuma Ibnu Taimiyya, wanda ya yi jika na kusan ɗari da Shehu Tijjani.

Haka Abul Hassan al-Ash'ariy da suke bi a Aƙida (duk da ya barranta daga ƙungiyar tasu), Imamu Ahmad bn Hanbal ya girme shi, nesa ba kusa ba.

Saboda haka da "Ash'ariyyancin", da "Sufancin", duka ba su ƙetare ƙarni na uku ba. A ƙarni na uku aka ƙirƙire su.

Amma Sunnar da Wahabiya suke kai kuma fa, ita kam daga kan Imamu Ahmad, da Shafi'iy da Malik da Abu Hanifa, ta tafi zuwa Tabi'ai, zuwa Sahabbai, ta tiƙe zuwa ga Manzon Allah (saw).

Saboda haka duka waɗannan ƙungiyoyin naku na bidi'a, ƴaƴan shegu ne, ba su da uba a cikin Addinin Muslunci. "Wahabiyanci" shi yake da Uba, shi yake da tushe a cikin Addinin Muslunci.

~ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

Previous Post Next Post