Mona Khalil, fitacciyar mai fafutukar kare muhalli kuma mai kare kunkuruwan teku a Lebanon, ta rasu sakamakon raunukan da ta samu bayan wani hari da Isra’ila ta kai kan gidanta a kudancin Lebanon.
Khalil ta shafe sama da shekaru 25 tana kare kunkuruwan teku masu fuskantar barazanar ɓacewa a gabar tekun Mansouri. Ayyukanta sun taimaka wajen mayar da yankin ya zama ɗaya daga cikin muhimman wuraren kare kunkuru a gabashin Tekun Bahar Rum.
An ji mata raunuka ne bayan wani harin sama na Isra’ila ya afka gidanta, wanda aka fi sani da “Orange House”, a farkon watan Yuni. Bayan kwanaki tana karɓar magani a asibiti, ta rasu sakamakon munanan raunukan da ta samu.
Mutuwarta ta jawo alhini daga masu kare muhalli, ‘yan jarida, masu fafutuka da mazauna Lebanon, inda da dama suka bayyana ta a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu kare muhalli da ƙasar ta taɓa samu.
An haifi Mona Khalil a birnin Lagos a shekarar 1949 ga iyalan Lebanon, kafin daga baya ta koma ƙasarta inda ta sadaukar da rayuwarta wajen kare namun daji da muhalli.
Masu sa ido sun ce rasuwarta babban rashi ne ga harkar kare muhalli a Lebanon da ma yankin baki ɗaya, musamman wajen kare kunkuruwan teku da sauran halittu masu fuskantar barazana.