Mutane Uku Sun Mutu Yayin Da Ukraine Da Rasha Sukai Musayar Hare-Haren Ketare Iyaka

 Mutane uku sun rasa rayukansu yayin da Ukraine da Russia suka ƙaddamar da hare-haren ƙetare iyaka kan juna a sabon rikicin da ya sake ruruwa tsakanin ƙasashen biyu. 

Ukraine da Russia

A yankin Bryansk na Rasha, jami'ai sun ce mutane biyu sun mutu sannan wasu biyu suka jikkata bayan harin da ake zargin sojojin Ukraine ne suka kai. 

A gefe guda kuma, a yankin Sumy na Ukraine, wata mata mai shekaru 44 ta mutu yayin da wani harin jirgin sama marar matuƙi (drone) da Rasha ta kai ya afku. Wata mata kuma ta samu raunuka a harin. 

Rahotanni sun nuna cewa bangarorin biyu sun ci gaba da kai hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami kan muhimman wurare, ciki har da cibiyoyin makamashi, tashoshin jirgin ƙasa, da sauran kayayyakin more rayuwa. 

Masana tsaro sun ce ci gaba da musayar hare-haren na nuna yadda yaƙin ke ƙara tsananta duk da ƙoƙarin da ake yi na ganin an dawo teburin tattaunawa domin samar da zaman lafiya. 

Rikicin da ya daɗe tsakanin Ukraine da Rasha ya ci gaba da haddasa asarar rayuka da lalacewar dukiyoyi, yayin da ƙasashen duniya ke kira ga ɓangarorin biyu da su rage tashin hankali tare da neman mafita ta diflomasiyya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post