NYSC Ta Haramta Tura Masu Bautar Kasa Zuwa Kananan Hukumomi Uku A Jihar Kebbi

Hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima ta kasa (NYSC) ta sanya kananan hukumomin Augie, Arewa da Sakaba na Jihar Kebbi cikin jerin wuraren da ba za ta sake tura masu yi wa ƙasa hidima ba saboda matsalar tsaro.

Masu Bautar Kasa

Kodinetan NYSC na jihar, Bala Dabo Kagarko, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a sansanin horaswa na wucin gadi da ke Basura a Karamar Hukumar Jega.

Ya ce hukumar ta kuma nemi a mayar da sansanin horaswa daga Dakingari zuwa Basura domin inganta tsaron masu bautar ƙasa.

Kagarko ya koka da cewa yawan masu yi wa ƙasa hidima da ake turawa jihar ya ragu sosai, lamarin da ya haifar da ƙarancin likitoci da malamai da ake tura wa asibitoci da makarantu.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu Kebbi ce jihar da ke karɓar mafi ƙarancin masu yi wa ƙasa hidima a faɗin Najeriya, duk da ƙoƙarin da aka yi na neman mafita daga hukumomin da abin ya shafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post