"Yabo Da Jinjina Ya Kamata Ƴan Arewa Su Yi Wa Rarara Domin Davido Ya Wofantar Da Arewa, Ya Nuna Wa Duniya Cewa Ƴan Kudu Ne Kaɗai Mutane A Nijeriya" In Ji Masu Sharhi.
Masu nazari da lura kan al'amuran yau da kullum a Najeriya sun bayyana cewa Rarara ya cancanci yabo da jinjina matuƙa kan sukar da ya yi wa Davido game da bayyana wa Duniya halin da Najeriya take ciki ta fannin tsaro. Domin kuwa, Davido da ya tashi jan hankalin Duniya kan matsalar ya nuna gata da tausayi a kan yara ɗalibai da aka sace a yankin Kudu kaɗai.
"Duk da cewa an jima ana kashe al'umma a Arewa, an kuma daɗe ana garkuwa da mutane ana sace ɗalibai da yara ƙanana a Jihohin Borno Zamfara Kebbi Sakkwato da sauransu, amma Davido bai nuna jimami a kansu ba sai da aka taɓa ƴan'uwansa ƴan Kudu". In ji su.
Masu sharhin sun kuma ƙara da cewa da ace Davido bai ɗauki ɓangare ba a abin da ya haska wa Duniya, to da ya haɗa da sunayen ɗalibai da mutanen da ke hannun masu garkuwa da mutane a Arewa, ko ya nuna wata alama da za ta fito da Arewa a san matsalar da take ciki.
Baya da haka, a cewarsu idan aka sake nazarin kalaman Rarara ta ɓangaren yadda ya zargi mutane da taimaka wa ƴanta'adda a Social Media ta hanyar yayata ayyukansu, za a fahimci cewa ba komai a cikin maganganun nasa face zallar gaskiya.
Domin kuwa sau da dama masu garkuwa da mutane ba su san wanda suka kama ba, amma yadda Media za ta ɗauka ana yaɗa hotuna da bayyana matsayin wanda aka kama ɗin a Arewa, shi ke ƙara wa ƴanta'addan ƙarfi har ta kai ga wasu da suka fi su ƙarfi sun je sun sari wanda aka kama ɗin kamar yadda Rarara ɗin ya ce hakan ta faru a kan mahaifiyarsa.
Sannan wata matsalar kuma, a wasu lokutan ƙarfin ƴan'ta'addan bai kai ba, amma yadda mutane suke ƙwarzanta ayyukansu a Social Media suke gani, hakan na ƙara musu izza da ƙara shiri, sannan sauran al'umma kan shiga fargaba, ana ƙara jefa tsoro a zukatan ƴan ƙasa.
Saboda haka, a fahimtarmu, Rarara ya yi abin yabo matuƙa da ya fito ya ja hankalin al'umma ya nuna musu illar yaɗa mutane idan an kama su, domin wasu da ba dan ana amfani da Social Media wajen nuna wa ƴan ta'adda matsayinsu a cikin al'umma ba da ba a sha wahala wajen ceto su, fanso su ko karɓo su ba, ƙila wasu ƴan ta'addar ne ma da kansu za su sake su saboda sun ga ba a kula su ba. Amma yawan zuzuta maganar ita ke ƙara sa wa su ci gaba da riƙe mutum tare kuma da ci gaba da ƙara kama wasu.
"Haƙiƙa Rarara ya yi abin yabo, muna yaba masa, muna jinjina masa. Sannan muna kira ga mutanen Arewa su mara masa baya su ƙarfafe shi kan wannan gagarumin namijin ƙoƙari da ya yi. Domin ya nuna wa Duniya cewa ba ƴan Kudu ne kaɗai mutane ba, Arewa ma tana da murya". In ji masu sharhin.
