Shuwagabannin G7 Za Su Karfafa Tsaron Sararin Samaniyar Ukraine Da Kara Tsaurara Takunkumi Kan Rasha

 Shuwagabannin ƙasashen Group of Seven (G7) sun bayyana shirinsu na ƙara tallafawa Ukraine ta hanyar ƙarfafa tsarin kare sararin samaniyarta daga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

Group of Seven (G7)

A yayin tarurrukansu, shugabannin sun tattauna hanyoyin ƙara taimakon tsaro ga Ukraine, musamman wajen samar da kayan kariya da fasahohin da za su taimaka wajen dakile hare-haren da ake zargin Russia na kaiwa.

Bugu da ƙari, ƙasashen G7 na shirin ƙara tsaurara takunkuman tattalin arziki kan Rasha domin ƙara matsin lamba a kanta dangane da rikicin da ke ci gaba a Ukraine.

Jami’an ƙasashen G7 sun ce manufar waɗannan matakai ita ce rage ƙarfin Rasha na ci gaba da yaƙi tare da tallafa wa Ukraine wajen kare yankunanta da al’ummarta.

Tun bayan fara rikicin, ƙasashen G7 sun kasance cikin manyan masu ba Ukraine tallafin kuɗi, kayan yaƙi, da taimakon jin ƙai, tare da kakaba wa Rasha jerin takunkumai a fannoni daban-daban.

Masana siyasa sun ce ƙarin tallafin tsaro da sabbin takunkumai na iya ƙara tsananta takun-saka tsakanin Rasha da ƙasashen yamma, amma kuma za su nuna ci gaba da goyon bayan da G7 ke bai wa Ukraine.

Ana sa ran shugabannin za su bayyana ƙarin cikakkun bayanai kan sabbin matakan a ƙarshen taron nasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post