Sojojin Amurka Ne Suka Dakatar Da Kisan Kiristoci A Nijeriya In Ji Donald J Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa sojojin Amurka sun taimaka wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya.

Donald J Trump

Trump ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a birnin Washington ranar Juma’a, inda ya ce matakan da Amurka ta ɗauka a Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen dakile hare-haren da ake zargin ana kai wa mabiya addinin Kirista a yankunan da ke fama da ta’addanci.

Ya ce kafin matakin, dubban mutane da suka haɗa da mata, yara da tsofaffi sun rasa rayukansu a hare-haren da ya bayyana a matsayin masu muni.

Trump ya kuma yi iƙirarin cewa hare-haren da Amurka ta kai sun raunana waɗanda ke da alhakin waɗannan kashe-kashe, yana mai cewa an kashe shugabanninsu da wasu manyan jagororinsu.

Sai dai shugaban na Amurka bai bayyana cikakkun bayanai kan lokacin ko irin ayyukan sojan da ya ce an gudanar a Najeriya ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post