Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa dakarun Operation Hadin Kai sun ceto mutane 360 da aka yi garkuwa da su daga wani sansanin Boko Haram da ke yankin tsaunukan Mandara a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Rundunar sojin ta ce an samu nasarar ceto su ne bayan wani gagarumin samame da aka shirya bisa bayanan sirri.
Wadannan mutanen na daga cikin mutane 416, ciki har da yara kanana, da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su lokacin da suka kai hari garin Ngoshe a watan Maris.
A lokacin harin, kungiyar ta fitar da wani bidiyon farfaganda inda wani kwamandanta ya yi ikirarin cewa za su ci gaba da rike garin Ngoshe har zuwa karshen watan Ramadan tare da gudanar da sallar Idi a Babban Masallacin Ngoshe.
Sai dai daga baya hare-haren fatattakar 'yan ta'adda da dakarun Operation Hadin Kai suka kai ya tilasta wa mayakan barin yankin. A ranar Eid-el-Fitr kuwa, dakarun sojin tare da mazauna yankin sun gudanar da sallar Idi lafiya a masallacin da kungiyar ta yi ikirarin mallakawa, lamarin da ya zama babban koma baya ga farfagandarta.
Yadda aka gudanar da aikin ceton
A cikin wata sanarwa da mukaddashin kakakin Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Haruna Sani, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce aikin ceton ya biyo bayan makonni na tattara bayanan sirri, sanya ido da kuma tsara farmakin.
A cewarsa, hukumomin tsaro sun samu sahihan bayanai da suka gano inda ake tsare da mutanen tare da gano hanyar sadarwa da masu taimaka wa 'yan ta'addan ke amfani da ita wajen tallafa wa sansanin.
Ya bayyana cewa jami'an leken asirin soji sun hada bayanan sirri daga mutane, na'urorin sadarwa da kuma jiragen sama marasa matuka domin nazarin yankin, bibiyar ayyukan 'yan ta'adda da kuma tantance halin da wadanda aka sace suke ciki.
Haruna Sani ya ce an samu eannan babban nasata ne bayan jami'an leken asiri sun samu damar kutsawa cikin hanyar sadarwar 'yan ta'addan, lamarin da ya ba su cikakkun bayanai kan inda aka boye mutanen, yadda kwamandojin kungiyar suka tsara kansu da kuma hanyoyin zirga-zirgar su.
Ya kara da cewa wasu dabaru na koluluwar sirri da jami'an tsaro suka yi ne ya kawo rudani a cikin kungiyar, lamarin da ya sa aka samu nasarar gaske a harin da aka kai.
An kai farmaki cikin dare
Bayan samun wadannan bayanai, dakarun sojin sun kaddamar da farmaki daga bangarori daban-daban cikin dare, inda suka killace yankin tare da toshe hanyoyin da mayakan za su iya bi wajen tserewa.
"Farmakin ya zo wa 'yan ta'addan ba-zata, wanda ya hana su shirya martani cikin lokaci," in ji kakakin rundunar.
A cewarsa, wasu daga cikin mayakan sun tsere zuwa tsaunukan da ke kewaye da yankin, yayin da wasu kuma suka mika wuya yayin da dakarun ke ci gaba da matsawa gaba.
Daga nan ne aka kwashe mutanen da aka ceto zuwa wurare masu tsaro, inda aka yi musu gwaje-gwajen lafiya tare da fara ba su kulawar jin kai da magunguna.
Jarirai biyu sun mutu
Sai dai Haruna Sani ya bayyana cewa jarirai biyu sun rasa rasu sakamakon gajiya da kuma mawuyacin yanayin tsaunukan da suka jure a lokacin da suke hannun masu garkuwa da mutane.
Ya bayyana aikin ceton a matsayin daya daga cikin manyan nasarorin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su da aka samu a yankin Arewa maso Gabas cikin 'yan shekarun nan.
A cewarsa, hedikwatar rundunar sojin ta yaba wa dakarun da suka gudanar da aikin, tana mai cewa nasarar ta nuna irin tasirin ayyukan tsaro da suka dogara da bayanan sirri da kuma kyakkyawar hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.
Ya kara da cewa ana ci gaba da wasu sabbin hare-haren fatattakar 'yan ta'adda domin kamo wadanda suka tsere, rusa sauran hanyoyin tallafi da suke amfani da su da kuma hana sake afkuwar irin wadannan sace-sacen mutane a yankin.
