Sojojin Tarayyar Nijeriya Sun Kwato Daliban Da Aka Sace A Jihar Borno

Sojoji sun ceto ɗalibai bakwai daga cikin waɗanda aka sace a harin da aka kai wata makaranta a Borno. Jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ‘yan sanda da kuma dakarun sa-kai na Civilian JTF sun ceto ɗalibai bakwai daga cikin waɗanda aka sace a harin da ‘yan ta’addar ISWAP suka kai makarantar sakandaren Lassa Day Secondary School da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.

Sojojin Tarayyar Nijeriya

Jaridar Punch ta rawaito cewa maharan sun kai harin ne da safiyar Litinin yayin da ɗalibai ke rubuta jarabawar NECO, inda suka riƙa harbe-harbe tare da yin awon gaba da wasu ɗalibai da mata ‘yan kasuwa da ke cikin harabar makarantar.

Kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida na jihar Borno, Usman Tar, ya tabbatar da ceto ɗaliban bakwai, yana mai cewa har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda aka sace.

Ya ce har yanzu ba a tantance adadin ɗaliban da aka sace ba, kuma gwamnatin jihar ta tura tawaga zuwa yankin domin tantance halin da ake ciki tare da kwantar da hankalin mazauna garin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, Nahum Daso, ya ce jami’an tsaro sun yi artabu da maharan, lamarin da ya hana su yin garkuwa da mutane da yawa.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da hare-hare kan makarantu ke ci gaba da ƙaruwa a yankin Arewa maso Gabas.

Post a Comment

Previous Post Next Post