Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar Japan ce ta fara jefa ƙwallo ɗaya a ragar Brasil, wadda hakan ya ba ta ƙarfin gwiwar ganin za ta fitar da ƙungiyar ta Brasil daga gasar cin kofin duniya.

Sai dai rashin sa'a ya sa Casemiro ya dasa wa ƙwallo kai ta shiga ragar Japan a mintina na 56, kafin daga bisani Gabriel Martinelli ya zura ƙwallo ta biyu a mintinan ƙarshe na wasan.
Wanda wannan ƙwallo ta zama silar korar Japan daga gasar cin kofin duniya, yayin da tawagar Brasil ta tsallaka zuwa rukunin 'yan 16.
A baya dai ƙungiyar Canada ce ta fara yin nasarar tsallakewa zuwa zagayen bayan da ta doke South Africa, yanzu kuma ga Brasil na take mata baya.