Shugaban ƙasar United States, Donald Trump, ya bayyana goyon bayansa ga ɗan majalisar wakilai Mike Collins a zagayen ƙarshe na zaɓen fidda gwani na kujerar Majalisar Dattawan Amurka (Senate) ta Jam’iyyar Republican a jihar Georgia.
Collins na fafatawa da tsohon kocin wasan ƙwallon ƙafa, Derek Dooley, domin samun tikitin jam’iyyar Republican da zai ba shi damar ƙalubalantar Sanata mai ci, Jon Ossoff, na Jam’iyyar Democrat a babban zaɓe.
A cikin sanarwar goyon bayan nasa, Trump ya yabawa Collins a matsayin amini kuma mai goyon bayan manufofinsa, tare da kira ga magoya bayan Republican a Georgia da su zaɓe shi.
Wannan goyon bayan ya zo ne kwanaki kaɗan kafin gudanar da zaɓen zagaye na biyu, kuma ana kallonsa a matsayin wani gwaji na irin tasirin da Trump ke ci gaba da da shi a cikin Jam’iyyar Republican.
Har ila yau, lamarin ya sake nuna bambancin ra’ayi tsakanin Trump da Gwamnan Georgia, Brian Kemp, wanda ake cewa yana goyon bayan Derek Dooley.
Masana siyasa sun ce sakamakon zaɓen zai iya nuna yadda masu zaɓe na Republican ke kallon ‘yan takarar da Trump ke mara wa baya, musamman a jihohin da ake ganin suna da muhimmanci a siyasar Amurka.
Ana ɗaukar wannan fafatawa a matsayin ɗaya daga cikin muhimman zaɓukan Majalisar Dattawa, domin sakamakonta na iya yin tasiri kan ƙarfin jam’iyyun siyasa a majalisar bayan zaɓe mai zuwa.
Masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce jihar Georgia na ci gaba da kasancewa muhimmiyar jihar da ke iya sauya alkiblar siyasar Amurka, wanda ya sa wannan zaɓe ya jawo hankalin jama'a da dama.