Wakar Makada Ibrahim Narambada Ta Sarkin Gobir Na Isa Malam Amadu Basharu

 "Sarki Kakanka yayi,

  Sarki Tsofonka yayi,

  Tau kai ko kayi Sarki,

  Gidan Basharun

   Ummaru sun sani,

   Koda baka nan su

   kayin Sarki".

Marigayi Malam Amadu Basharu

Cewar Makaɗa Alh. (Dr.) Ibrahim Narambaɗa Tubali☝️ a wata waƙar babban ubangidansa, Sarkin Gobir na Isa Marigayi Malam Ahmadu Basharu (Ahmadu Bawa/Ahmadu I) mai amshi "Amadun Bubakar gwarzon Yari,  Dodo na Alkali".

Duk da yake hotunan dake tare da wannan rubutu nawa basu da alaƙa da wannan waƙar amma labarin da waƙar ta taskace yayi kama da nasu idan muka yi la'akari da yadda Allah SWT ya tsara masu rayuwa tamkar irin yadda ya tsarawa wanda aka yiwa waƙar.

A Masarautar Ƙauran Namoda da Muzaffar Muhammadu Namoda ya ƙirƙira a shekarar 1807 ta kuma zama garin Ribaɗi ga masu jihadin jaddada addinin Musulunci na Daular Usmaniyya a cikin ƙarni na 19 an samu irin abin da Makaɗa Narambaɗa Tubali ya ambata a fadar Isa dake cikin wannan waƙar.

Ya ambaci Basharun Ummaru, kenan yana nufin Sarkin Gobir na Isa Basharu ɗan Sarkin Gobir na Isa Ummaru ɗan Sarkin Musulmi Aliyu Karami ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo Tagammadahullah Birahamatihi.

Sarkin Gobir Ummaru shi ne mahaifin Sarkin Gobir Basharu, Sarkin Gobir Basharu shi ne mahaifin Sarkin Gobir Ahmadu Bawa/Ahmadu I wanda ya yiwa wannan waƙa. Ta tabbata kakan Ahmadu Bawa wato Umaru ɗan Sarkin Musulmi Aliyu Ƙarami ya yi sarautar Sarkin Gobir na Isa, mahaifinsa(Sarkin Gobir Ahmadu I /Ahmadu Bawa) wato Basharu ɗan Ummaru ya yi sarautar Sarkin Gobir, to shi ma ya zama Sarkin Gobir na Isa a shekarar 1935/36.

A Ƙauran Namoda Alhaji Ahmad Muhammad Asha ya zama Sarki a shekarar 1960 har zuwa wafatinsa a shekarar 2004. Ɗansa Muhammad Ahmad Asha ya gaje /gade shi, ya yi sarauta daga shekarar 2004 har zuwa rasuwarsa a shekarar 2020, shi kuma ɗansa Alh. Sanusi Muhammad Ahmad Asha ya gaje/gade shi, shi ke sarauta ya zuwa yau.

Batun Narambaɗa ya fito a wannan bagire domin kuwa kakan Sarkin Kauran Namoda na yanzu shi ne Sarki Ahmadu ɗan Sarki Muhammadu Asha dan Sarki Basharu. Sarki Ahmadu ɗan Sarki Muhammadu Asha shi ne ya haifi Sarki Muhammadu Ahmadu wanda shi ne ya haifi Sarki Sanusi Muhammadu Ahmadu Asha.

Kakansa da Tsofonsa sun yi sarauta shi ma gashi Allah SWT ya ƙaddare shi da zama Sarki, kenan kamar yadda Makaɗa Narambaɗa Tubali ya ambatawa Sarkin Gobir na Isa Ahmadu Basharu /Ahmadu Bawa/Ahmadu I gashi nan an samu kwatankwancin haka a Tarihin rayuwar mai martaba Sarkin Kiyawan Kauran Namoda, Alh. Sanusi Muhammad Ahmad Asha.

Allah ya jiƙan dukan magabatanmu ya ƙarawa mai martaba Sarki lafiya ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.

  Na farko a gefen hagu a cikin wannan hoto shi ne Marigayi mai martaba Sarkin Kiyawan Kauran Namoda, Alh. Ahmad Muhammad Asha, a tsakiya ɗansa ne Marigayi mai martaba Sarkin Kiyawan Kauran Namoda Alh. Muhammad Ahmad Asha sai jikansa, mai martaba Sarkin Kiyawan Kauran Namoda na yanzu, Alh. Sanusi Muhammad Ahmad Asha dake farko a hannun dama na hoton. 

Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji), Jihar Zamfara, Nijeriya.

28/06/2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post