Yanbindiga Sun Sace Daliban Makarantar Kaura Namoda Polytechnic A Zamfara

Rundunar ƴansanda a Najeriya ta ce ƴanbindiga sun sace wasu ɗaliban kwalejin fasaha ta tarayya da ke Ƙaura Namoda a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Yanbindiga

An sace ɗaliban bakwai da sanyin safiyar jiya Laraba daga gidan da suke zaune a yankin Kaura Namoda

Kakakin rundunar ƴansandan jihar Yazid Abubakar cikin wata sanarwa ya ce maharan sun kutsa gidajen ɗaliban inda kuma suka yi awon gaba da wasu daga cikinsu.

Sanarwar ta ƙara da cewa an tuntuɓi sojoji da jami'an da aka tura yankin sai dai ƴanbindigar sun riga sun tsere kafin jami'an tsaro su isa wajen.

"Ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace ya samu tserewa kuma tuni aka miƙa shi ga hukumomi yayin da ake ƙara ƙoƙari na gano ragowar mutum shida," in ji sanarwar.

Rahotanni sun ce jami'an tsaro tuni suka fara samame domin gano inda ƴanbindigar suke kuma zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.

Jihar Zamfara da Kebbi da Katsina masu maƙwabtaka na fuskantar ƙaruwar hare-hare a baya-bayan nan sakamakon ayyukan ƴanbindiga.

Post a Comment

Previous Post Next Post