Rahotanni suna nuna cewa ana sa ran mummunan yanayin zafi zai addabi sassan Yammacin Turai a yau Talata, inda zafin zai kai matakin da aka daɗe ba a gani ba a tarihi.
Masana hasashen yanayi sun ce zafin zai ƙara tsanani a wannan makon lamarin da ke haddasa fargaba a ƙasashe da dama.A Faransa, an gargaɗi sama da rabin ƴan ƙasar kan mummunan yanayin zafi yayin da aƙalla mutane 18 ne suka mutu sakamakon zafin a ranar Litinin.
A Birtaniya ma ana sa ran za a fuskanci mummunan yanayin zafi a tarihi a wannan watan na Yuni, inda yanayin zafi zai iya haura digiri 35 a ma’aunin Celsius.
Haka kuma a Spain da Portugal, yanayin zafi ya wuce yadda aka saba gani a daidai irin wannan lokaci na shekara, inda wasu yankuna ke fuskantar ƙarin yanayin zafi mai tsanani.