Dan majalisar dokokin Iran mai wakiltar Tehran, Kamran Ghazanfari, ya sanar da shirin gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar kasar domin nuna adawa da rufe majalisar da aka yi na tsawon watanni.
A wani sako da ya wallafa a shafin X, Ghazanfari ya ce wasu daga cikin ‘yan majalisa za su je ginin majalisar da karfe 8 na safe a ranar Lahadi.Ya ƙara da cewa idan har suka tarar majalisar a rufe, za su zauna a wajen a matsayin zaman dirshan har sai an sake buɗe ta.
Dan majalisar ya bayyana kiran nasa ne ga al’ummar Iran, yana mai jaddada cewa rufe majalisar na dogon lokaci ba abin da ya dace ba ne.