An Nuna Damuwa Kan Yadda Kuɗi Ke Mamaye Siyasar Nijeriya, Ana Hana Masu Ƙwarewa Samun Mulki

Mai shirya taron Leadership Renaissance Forum, Dakta Robert Abdullahi Johnson, ya bayyana damuwarsa kan yadda neman mukaman siyasa a Nijeriya ke ƙara zama abin da ya dogara da kuɗi, yana mai gargadin cewa hakan na hana ƙwararru da masu hangen nesa samun damar jagoranci saboda rashin isassun kuɗaɗen fafatawa.

Johnson ya ce tsadar neman mukaman siyasa da ke ƙaruwa tana haifar da tsarin da ke fifita masu kuɗi maimakon masu cancanta, lamarin da ke sa mutane masu basira da ƙwarewar da za su iya kawo sauyi a ƙasar su kasa fitowa a matsayin shugabanni.

Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron Leadership Renaissance Forum mai taken “Sake Tunanin Jagoranci Domin Ci Gaban Ƙasa”, wanda aka shirya domin ƙarfafa tunani mai kawo sauyi da kuma inganta jagoranci mai manufa a Nijeriya da Afirka baki ɗaya.

A cewarsa, matsalolin ci gaban da Nijeriya ke fama da su ba su samo asali ne daga ƙarancin albarkatu ba, sai dai daga rashin nagartaccen shugabanci da kuma tsarin siyasar da ke yawan ware mutanen da suka cancanta.

“Babu wata matsala da ƙasar Nijeriya take da ita. Babu matsala da ƙasarmu, yanayinmu ko albarkatunmu. Nijeriya ƙasa ce mai albarka. Duk da haka muna ci gaba da fuskantar koma baya saboda rashin kyakkyawan shugabanci,” in ji shi.

Johnson ya jaddada cewa shugabanci shi ne ginshiƙi mafi muhimmanci wajen ci gaban kowace ƙasa, yana mai cewa ci gaba ko koma bayan al’umma ya danganta ne da ingancin mutanen da aka ɗora wa nauyin jagoranci.

Ya kuma yi tir da yadda mutane da dama da ke riƙe da muƙaman jagoranci a fannoni daban-daban ba su da cikakken shiri da cancantar gudanar da nauyin da ke kansu, lamarin da ke haifar da gazawa a harkokin mulki da ci gaban ƙasa.

“Manufarmu ita ce ilmantar da shugabanni da kuma gina nagartaccen shugabanci. Kamar yadda masana shugabanci suka sha faɗi, komai yana tashi ko faɗuwa ne bisa ingancin shugabanci,” in ji shi.

Masanin ya kuma bayyana cewa nagartattun shugabanni ba sa bayyana ne kawai ba tare da tsari ba, sai an gano su, an horar da su kuma an ba su goyon baya daga al’umma.

Ya ƙara da cewa yanayin siyasar da ake ciki yanzu ya sa samun mukaman gwamnati ya fi dogaro da ƙarfin kuɗi maimakon cancanta, mutunci da hangen nesa.

“An cusa kuɗi sosai cikin tsarin neman mukaman siyasa. Namiji ko mace mai iya kai Nijeriya ga babban matsayi na iya rasa damar fitowa saboda ba shi da isassun kuɗaɗen da za su ba shi damar bayyana kansa ko tsallake matakan siyasa,” in ji Johnson.

Post a Comment

Previous Post Next Post