2027: Gwamnan Kaduna Uba Sani Ya Aiyana Jerry Adams a Matsayin Mataimakinsa a Takara

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Jihar Kaduna (KADIRS), Jerry Adams, a matsayin wanda zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi a zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Uba Sani

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Uba Sani ya ce zaɓin Adams ya yi daidai da manufofin gwamnatinsa na adalci, haɗin kai da kuma bai wa kowa dama ba tare da nuna bambanci ba.

Gwamnan ya bayyana Jerry Adams a matsayin gogaggen jami'in gwamnati kuma ƙwararre a harkar haraji, yana mai cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta aikin KADIRS, lamarin da ya ƙara wa jihar kuɗaɗen shiga na cikin gida tare da ba gwamnati damar zuba jari a fannonin ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da noma.

Uba Sani ya yi kira ga al'ummar Kaduna da su mara wa tikitin baya, yana mai jaddada cewa a duba wannan zaɓi a matsayin matakin ƙarfafa haɗin kai da ci gaban jihar, ba tare da la'akari da bambancin addini, ƙabila ko yanki ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post