Shugabannin yankin Arewa maso Gabas sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaben 2027, tare da alkawarin tattara kuri’un yankin ga jam’iyyar APC.
Gwamnoni, ministoci, ’yan majalisa, sarakuna da dattawan jihohin Borno, Adamawa, Bauchi, Gombe, Taraba da Yobe ne suka kai wa Tinubu ziyarar godiya a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. Ziyarar ta biyo bayan matakin Tinubu na sake zaben Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.
Gwamnan Borno kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas, Farfesa Babagana Zulum, ya ce matakin ya nuna yadda shugaban kasa ke daraja biyayya, kwarewa da sadaukarwa. Ya ce ci gaba da barin Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa ya kara wa yankin kwarin gwiwa.
Zulum ya yaba wa gwamnatin Tinubu kan ayyukan hanyoyi, noma, ilimi, tallafa wa matasa da kuma kula da ’yan gudun hijira a yankin. Ya tabbatar wa shugaban kasa cewa shugabanni da magoya bayan APC a Arewa maso Gabas za su hada kai domin tabbatar da nasarar Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar a 2027.
Da yake mayar da martani, Tinubu ya ce goyon bayan da yankin ya nuna abin faranta rai ne, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta tattalin arziki, tsaro da hanyoyin mota. Ya ce hadin gwiwar gwamnatin tarayya da jihohi na da muhimmanci wajen yaki da ta’addanci da fashi da makami, tare da tabbatar da zaman lafiya da walwalar ’yan Najeriya.
