Isra'ila da Asusun Tallafa wa Ilimin Manyan Makarantu (TETFund) sun sake jaddada ƙudurinsu na bunƙasa masu ƙirƙire-ƙirƙire a Najeriya ta hanyar ƙarin zuba jari, bayar da horo, da musayar fasaha. Haka kuma, sun sanar da samar da kuɗaɗen gudanar da zagaye na biyar na shirin Innovation Fellowship for Aspiring Inventors and Researchers (iFAIR 5), tare da ƙara ƙoƙarin mayar da binciken da ake yi a jami'o'in Najeriya zuwa kayayyakin kasuwanci.
An bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin bikin rufe shirin iFAIR Cohort 4 da kuma Gasar Baje Kolin Ƙirƙire-Ƙirƙire da aka gudanar a Abuja, inda mahalarta suka nuna samfuran da suka ƙera a fannoni kamar noma, kiwon lafiya, makamashi mai tsafta da hanyoyin magance matsalolin al'umma.
Jakadan Isra'ila mai barin gado a Najeriya, Michael Freeman, ya sanar da cewa an riga an tabbatar da kuɗaɗen gudanar da iFAIR 5, wanda za a ƙaddamar da shi a watan Oktoban shekarar 2026.
"Ina alfahari da tsayawa a gabanku a yau domin sanar da cewa tare da abokan hulɗarmu mun tabbatar da kuɗaɗen gudanar da iFAIR 5, kuma za a ƙaddamar da shirin a watan Oktoba na shekarar 2026," in ji Freeman.
Freeman ya bayyana cewa wannan shi ne babban taronsa na ƙarshe kafin ya kammala wa'adinsa na shekaru huɗu da rabi a matsayin jakadan Isra'ila a Najeriya. Ya ce shirin iFAIR ya zama wata alama ta ƙarfafa haɗin guiwar ƙasashen biyu a fannin ƙere-ƙere da fasaha.
Ya jaddada cewa manufar shirin ba ita ce kawo hanyoyin warware matsalolin Isra'ila zuwa Najeriya ba, illa taimaka wa hazikan 'yan Najeriya su samar da mafita ga matsalolin ƙasarsu tare da amfani da gogewa, jagoranci da fasahar Isra'ila.
"Wannan shiri bai taɓa kasancewa domin kawo mafitar Isra'ila zuwa Najeriya ba. Manufarsa ita ce taimaka wa ƙwararrun masu ƙirƙire-ƙirƙire na Najeriya su samar da mafita ta Najeriya ga matsalolin Najeriya, tare da tallafin gogewa da jagoranci daga Isra'ila," in ji shi.
Ya ƙara da cewa shirin ya haɗa jami'o'i, gwamnati, masu zuba jari, injiniyoyi da 'yan kasuwa domin sauya kyawawan tunani zuwa kasuwanci, kasuwanci zuwa ayyukan yi, sannan ayyukan yi su zama ginshiƙin bunƙasar tattalin arziki.
Freeman ya ce a lokacin aikinsa, Najeriya da Isra'ila sun ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni da suka haɗa da kula da albarkatun ruwa, kiwon lafiya, ilimi da fasaha. Ya kuma gode wa Babban Sakataren TETFund, Sonny Echono, da cibiyar Innov8 Hub saboda ci gaba da tallafa wa shirin.
Ya ƙarfafa mahalarta da suka kammala shirin su ci gaba da jajircewa wajen ƙirƙirar mafita da za ta kawo sauyi a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.
"Najeriya na buƙatar masu ƙirƙire-ƙirƙire irin ku. Afirka na buƙatar ku. Haka ma duniya baki ɗaya na buƙatar ku," in ji Freeman.
A nasa jawabin, Babban Sakataren TETFund, Sonny Echono, ya ce shirin ya yi daidai da manufofin ci gaban Najeriya, musamman wajen tallafa wa ƙirƙire-ƙirƙire a fannoni kamar tsaron abinci, noma, kiwon lafiya, makamashi mai tsafta da tattalin arzikin sake amfani da albarkatu.
Ya bayyana cewa babban ƙalubalen da TETFund ke ƙoƙarin magancewa shi ne yadda za a mayar da sakamakon bincike da ƙirƙire-ƙirƙiren jami'o'i zuwa kayayyaki da za su shiga kasuwa, ta hanyar haɗa jami'o'i, gwamnati da masana'antu.
Echono ya kuma bayyana cewa TETFund na kafa cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire a manyan makarantu sama da 60 a faɗin Najeriya domin bai wa ɗalibai damar samar da mafita ga ƙalubalen ƙasa da na duniya tun suna karatu.
Ya yabawa Jakada Freeman bisa rawar da ya taka wajen ƙarfafa alaƙar Najeriya da Isra'ila, tare da ƙarfafa matasa masu ƙirƙire-ƙirƙire da su yi amfani da damar da shirin ke bayarwa wajen mayar da tunaninsu zuwa kasuwanci masu ɗorewa.
Wakilin Innov8 Hub ya ce Najeriya ba ta da ƙarancin hazaka, sai dai tana buƙatar ingantattun hanyoyi da za su sauya kyawawan dabaru zuwa kayayyaki, kasuwanci da damar tattalin arziki.
Ya bayyana cewa cibiyar ta tallafa wa sama da masu bincike, masu ƙere-ƙere da 'yan kasuwa 3,000, tare da taimakawa wajen ƙera sama da garkuwar fuska 10,000 a cikin gida lokacin annobar COVID-19.
Ya shawarci mahalarta shirin da su kasance kusa da masu amfani da kayayyakinsu, tare da mai da hankali kan samar da mafita ga ainihin matsalolin da al'umma ke fuskanta.
Shi ma wanda ya kafa Future Africa, Iyinoluwa Aboyeji, ya ce wajibi ne Najeriya ta rungumi Basirar Wucin Gadi (Artificial Intelligence - AI) da kuma musayar fasaha domin ƙara yawan aiki da kauce wa durƙushewar tattalin arziki.
Ya yabawa tsarin haɗin guiwar Isra'ila, yana mai cewa yana bai wa 'yan Najeriya ilimi da ƙwarewar gina fasahohinsu maimakon dogaro da kayayyakin da aka kammala daga ƙasashen waje.
Tun da farko, Shugabar Shirye-shirye ta iFAIR, Tolulope Aina, ta ce mahalarta Cohort 4 sun samu nasarar ƙera samfuran da ke magance matsaloli a fannonin noma, kiwon lafiya, makamashi da ci gaban al'umma, sakamakon haɗin gwiwa da injiniyoyin Najeriya da Isra'ila.
Ta yabawa masu ba da horo daga Isra'ila saboda jajircewarsu wajen tafiya tare da mahalarta har zuwa kammala ayyukansu.
"Samfuran da kuke gani a yau su ne farkon tafiya. Yanzu abin da ya rage shi ne ku kai su kasuwa domin su zama kayayyakin da za su amfani al'umma," in ji Aina.
Haka kuma, Shugaban Sashen Tasiri na Innov8 Hub, Olawale Balogun, da Babbar Daraktar Engineers Without Borders Israel, Michal Hashimshony, sun yaba wa mahalartan saboda nuna yadda injiniya da fasaha za su iya kawo sauyi mai amfani ga rayuwar jama'a.
Hashimshony ta ce fasaha dole ne ta kasance tana bauta wa bil'adama tare da warware matsalolin rayuwa na zahiri. Ta kuma yabawa yadda mata suka taka muhimmiyar rawa a fannin injiniya da ƙirƙire-ƙirƙire, tana mai cewa hakan na daga cikin abubuwan da suka fi burge ta a shirin.
Shirin iFAIR haɗin gwiwa ne tsakanin Ofishin Jakadancin Isra'ila, TETFund da Innov8 Hub, wanda ke tallafa wa masu ƙirƙire-ƙirƙire na Najeriya ta hanyar ba su horo, jagoranci, ƙwarewar injiniya, damar samun tallafi da kuma hanyoyin kasuwantar da bincike domin mayar da sabbin ra'ayoyi zuwa kayayyakin da za su shiga kasuwa.