Idan Kana Da Hujjar Da Za Ta Nuna Ni A Matsayin Mai Cin Hanci Da Rashawa Ka Matso Ka Fallasa Ni

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya jefa wani babban ƙalubale ga ɗaukacin al'ummar ƙasar Nijeriya, inda ya ce: "Ban cire wa kowa hula ba, duk wanda ya san yana da wata hujja da zai tabbatar wa da duniya cewa ya taɓa ganina ko kama ni da laifin cin hanci to ya matso kusa ya fallasa ni."

Ɗan takarar shugaban ƙasar ya bayyana wannan kalaman ne a shafinsa na X, wanda aka fi sani da Twitter a da.

Da yawan lokuta ba a cika jin irin waɗannan maganganun daga bakin 'yan siyasa ba, duba da cewa da yawansu suna ɗauke da wani abin da ya shafi cin hanci ko rashawa. 

A baya dai kafin rasuwarsa, Tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammad Buhari kusan dai shi kaɗai ne wanda har ya kammala wa'adin mulkinsa na soji da na farar hula na shugabancin ƙasar nan, wanda kai tsaye ba a same shi da wata almundahana ta cin hanci ko rashawa ba. To kuma kwatsam yau sai ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC ya zo da wata sabuwa.

Anya kuna ganin wannan ƙalubalen da Atiku Abubakar ya jefa zuwa ga al'umma, kuna ganin zai sha kuwa? Duba da cewa ya riƙe manyan muƙamai a ƙasar?

Post a Comment

Previous Post Next Post