MA'AIKATAR TSARO TA KASA, TA YI ALKAWARIN SAKE GINA JAMI'AR SOJIN NIJERIYA A BIU (NAUB)

Ma'aikatar Tsaron Ta Ƙasa Ta Yi Alƙawarin Sake Gina Jami'ar Sojin Najeriya Biu (NAUB)

Mai Girma Ministan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Musa (Mai Ritaya) OFR, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kuduri aniyar sauya Jami'ar Sojin Najeriya Biu (NAUB) zuwa cibiya ta gaba-gaba wajen horar da sojoji da farar hula.

Janar Musa ya bayyana haka ne a lokacin da yake karɓar baƙuncin Majalisar Gudanarwar Jami'ar a hedikwatar ma'aikatar da ke Abuja. Ya ce jami'ar na da matuƙar muhimmanci wajen ba ma'aikatan tsaro ilimin fasaha da ƙwarewar da za su taimaka wajen magance ƙalubalen tsaron da ƙasa ke fuskanta a yanzu.

Ministan ya kuma bayyana cewa ma'aikatar za ta yi aiki tare da Sojojin Najeriya domin tabbatar da cewa an cika kashi 30% na kujerun shiga jami'a da aka keɓe wa ma'aikatan soji.  
Ya ce: "A wannan zamanin na fasaha, dole ne mu ƙarfafa gwiwar sojoji, ma'aikatan gwamnati da jama'a gabaɗaya su yi amfani da sabbin dama da NAUB ke bayarwa."

A sakamakon taron, Ministan da Majalisar Gudanarwa sun cim ma yarjejeniya kan gaggawar gyara kayayyakin more rayuwa na jami'ar. Daga cikin manyan ayyukan da aka amince za a fara shi ne ginin "Centre for Military Performance Management" na zamani, wanda zai zama na farko irinsa a fadin nahiyar Afirka.

A nasa jawabin, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (Mai Ritaya) CFR, wanda shi ne Pro-Chancellor na farko na NAUB, ya yaba wa Ministan bisa jagoranci da hangen nesa. Ya ce sadaukarwar Janar Musa na ƙara ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar.

Ya kuma tabbatar wa Ministan cewa al'ummar jami'ar za su ci gaba da himmatuwa wajen tabbatar da ingancin ilimi, bincike da hidima ga ƙasa.

Rahoton: Leah Katung-Babatunde
Mataimaki na Musamman kan Watsa Labarai ga Ministan Tsaron Ƙasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post