Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar mataki kan Tarayyar Turai (EU), bayan da Brussels ta ci kamfanin Google tarar kusan dala biliyan 1 saboda zargin karya dokokin gasar kasuwanci na dijital na EU.
Hukumar Tarayyar Turai ta ci Google tarar Yuro miliyan 890, kwatankwacin kusan dala biliyan 1. Ta zargi kamfanin da fifita wasu daga cikin ayyukansa a sakamakon binciken Google, da kuma takaita wasu ‘yan kasuwa daga tura kwastomominsu zuwa wasu hanyoyin sayayya masu rahusa ta Google Play.
Trump ya yi kakkausar suka ga matakin na EU, yana zargin ƙungiyar da nuna wariya ga manyan kamfanonin fasahar Amurka. Ya kuma ce Amurka za ta fara wani sabon bincike kan manufofin cinikayyar EU da abin da ya kira “kwace” wa kamfanonin Amurka kuɗaɗensu.
Trump ya gargadi Tarayyar Turai cewa za ta “biya babban farashi” saboda matakin, sannan ya yi barazanar yi mata amfani da wani babban ƙarin haraji.
Wannan rikici ya ƙara tsananta rashin jituwar cinikayya tsakanin Amurka da Tarayyar Turai, musamman kan yadda Brussels ke ɗaukar matakan ladabtarwa kan manyan kamfanonin fasahar Amurka.