Abokai Biyu Sun Yi Fada A Wasan Zagayen 'Yan 16 Na Gasar Cin Kofin Duniya

A wasan da aka fafata juya tsakanin Spain da Portugal an hango yadda Bernardo Solve ya miƙe zumbur tare da tunkarar abokinsa Rodri wanda suke taka leda a ƙungiya ɗaya ta Manchester City a Ingila da nufin su ba hanmata iska.

Sai dai 'yan wasan da ke kusa a lokacin da abin ya faru, sun rirriƙe shi, inda suka hana shi isa kusa da Rodri, yayin da shi kuma Rodri y kasashe da dariya, tare da ƙoƙarin ba shi haƙuri kan abin da ya aikata masa. Amma Bernardo Silva ya yi fushi tare da buge hannunsa daga jikinsa.

Bayan an tashi wasan, Rodri ya bayyana cewa: "Na ba wa Silva haƙuri, saboda ni na yi murna a lokacin da ya sa wa ƙwallo kai ta yi waje, na san wannan ne zai ba shi haushi."

Shin kuna ganin alaƙa mai daɗi za ta ƙara ƙulluwa tsakanin 'yan wasan biyu? Duba da cewar akwai haushin an cire su a gasar. Sai dai duk da haka abin zai zo da sauƙi kasancewar Silva zai bar ƙungiyar ta City bayan kammala wasannin cin kofin duniya ya koma ƙungiyar Madrid da ke Sifaniya.

Irin wannan saɓanin dai ba yau aka fara samun ba, domin a baya ma, an taɓa samun irin sa a lokacin wasan Ingila da Portugal, wasan da Portugal ta kori Ingila, inda Ronaldo ya yi murnar da ta wuce misali. Wadda har Ronaldo da Rooney suka samu saɓani a lokacin, kuma hakan ya shafi zamantakewarsu har zuwa wannan lokacin.

Post a Comment

Previous Post Next Post