Bayan shekaru 24 da wata 10 da Anthony Taylor ya shafe yana alƙalancin wasanni, wanda ya fara alƙalanci a wasan ƙwallo tsakanin Wrexham da Peterborough, ya kuma rufe shi da wasan da ƙasar Spain 1-0 ta yi nasara akan Portugal a gasar cin Kofin Duniya na wannan shekarar. Alƙalin ya bayyana ajiye aikinsa domin komawa gefe ya ba wa matasa masu tasowa dama.
Anthony Taylor, ɗan shekaru 47, an haife shi a garin Wythenshawe da ke Manchester, ya sanar da ritaya daga alƙalancin wasa, kwanaki kaɗan bayan kammala wasansa na ƙarshe a gasar cin kofin duniya.
FARKO: 0-0 A WREXHAM, 2006
Da farko tafiyar Taylor ba ta fara da haske ba, inda ya fara bayyana a matsayin alƙalin wasa a Agusta ta shekarar 2006, a filin Racecourse Ground. Alƙali matashi ne ya bayyana yana riƙe da mabusa a wasan da Wrexham da Peterborough United suka yi canjarsa 0 - 0a gasar League Two.
Kafin nan ya shafe shekaru 4 yana alƙalanci a Northern Premier League da Conference North tun shekarar 2002. Sai dai ba wanda ya san wannan saurayin zai kai har matakin alƙalin da FIFA za ta kira ya yi alƙalanci a gasar cin kofin duniya ba.
Bayan wasu shekaru 4, 3 ga Fabrairu 2010*, Taylor ya sami damar da ya daɗe yana jira. Inda ya fara alƙalancin wasa na farko a Premier League tsakanin ƙungiyar Fulham da Portsmouth, wasan da aka tashi 1-0, inda Fulham ta yi nasara.
Daga nan aka ɗaga shi zuwa "Select Group" rukunin mafi kyawun alƙalai 20 a Ingila. A shekarar 2013, FIFA ta ɗauke shi, sannan sai aka fara ganin sunansa a manyan wasanni.
Wasu Daga Cikin Fitattun Wasannin Da Ya Yi Alƙalanci Sun Haɗa Da:
1. Wasan zagayen ƙarshe na gasar cin kofin FA Cup sau 2, a shekarar 2017 da 2020.
2. Sai wasan zagayen ƙarshe na gasar League Cup a shekarar 2015 da kuma wasan ƙarshe na cin kofin Community Shield a shekarar 2015.
3. Anthony Taylor ya yi alƙalanci a wasan ƙarshe na Europa League a shekarar 2023 tsakanin ƙungiyar Sevilla da A.S Roma
4. Ya kuma yi alƙalanci a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Zakarun Turai (Champions League) Wanda aka the 2023 tsakanin ƙungiyar Manchester City da Inter Milan
Anthony Taylor ya yi alƙalanci na ƙarshe a ranar 6 ga Yuli, 2026 a gasar cin kofin duniya a rwasannin rukunin 'yan 16, wanda aka fafata tsakanin Sifaniya da Portugal inda Sifaniya ta samu nasara a kan Portugal da ci 1 da nema 0. Wasan da Michel Merino ya zuri'a ƙwallon a raga bayan mintina kaɗan da shigowarsa filin.
A gabaɗaya rayuwar alƙalancinsa ya yi alƙalanci a wasanni 831 a cikin aikinsa, wanda wasanni 432 daga cikinsu duk a Premier League ya yi su.
A cikin shekaru 16 da ya yi yana alƙalanci a gasar cin kofin Premier League, Taylor ya bayar da katin gargaɗi (Yellow Card) sau 121.
Howard Webb, shugaban alƙalai na PGMOL, ya ce: "An daɗe da amincewa da shi a matsayin alƙalin da zai riƙa alƙalanci a manyan wasanni. Portugal da Spain a Kofin Duniya ne suka rufe aikinsa mai ban mamaki".
Wasu Daga Cikin Kalaman Anthony Taylor Bayan Ya Ajiye Aikin Alƙalancin Wasa: "Ina so in bayyana godiya ta ga mataimakaina biyu Gary Beswick da Adam Nunn, abokan aikina alƙalai, da duk wanda ke da alaƙa da wasan ƙwallo bisa goyon bayansu shekaru da masu yawa. Mafi mahimmanci, ina godiya ga iyalina da abokaina bisa goyon bayansu da ba ya raguwa tare da sadaukarwarsu na tsawon wannan lokaci.