Shugaban gasar ƙwallon ƙafa ta Spain (La Liga), Javier Tebas, ya zargi FIFA da ɗaukar matakan da za su iya lalata harkar ƙwallon ƙafa, bayan tattaunawar faɗaɗa gasar cin Kofin Duniya ta 2030 zuwa ƙasashe 64.
A wata hira da jaridar wasanni ta Italiya, Tebas ya ce FIFA na fifita gasar da ke ɗaukar kwanaki 40 kacal, tare da yin watsi da gasannin cikin gida da ke samar da dubban guraben aiki a duniya.
Ya kuma ce tsarin shugabancin FIFA ƙarƙashin Gianni Infantino ya gaza, yana mai cewa lokaci ya yi da zai sauka daga shugabancin hukumar.
Tebas ya jaddada cewa gasannin cikin gida ne ke raya ƙwallon ƙafa, yana mai kira da a rage yawan ƙasashen da ke shiga gasar cin Kofin Duniya tare da ba wa gasannin cikin gida kariya. Ya zargi FIFA da yanke hukunci ba tare da la'akari da illolinsa ga harkar ƙwallon ƙafa ba.
