RIGA BA WUYA
Assalamu alaikum 'yan'uwa,
Ga ni ɗauke da saƙo ba wuya.
Ya Allah sarkin duniya,
Dabba aljan da mutaniya.
Khaliƙin sammai da ƙasan bakwai,
Khaliƙi na halittun duniya.
Na yi roƙo gun ka maɗaukaki,
Taimake ni ya zam ni zan iya.
Tura saƙo lungu saƙuna,
Ya karaɗe dukkan nahiya.
'Yan birni har ma karkara,
Na dukan lardojin duniya.
Na zo kaina tsaye ba kwana,
In sake faɗa maku gaskiya.
Bandits 'yan iskan unguwa,
Sun hana mu sakat a gidan iya.
Sun ƙone gida da su rumbuna,
Inda mun ka aje kayan miya.
Sun ɓarke gida, sun ɗau mutum,
Har shanu ba sa shariya.
Mata da maza, yara duka,
Ba su bar komai ba ya wataya.
Ke gwamnati kullum sai ki ce,
Everything under control.
Amma dai zancen gaskiya,
Wannan zancen kwai tariya.
Ba inda yake bisa control,
Balle mu yi barcin safiya.
Har gobe da jibi ina faɗa,
Gayun nan ga su a midiya.
Ka gan su a can, har ma da nan,
Har live ba su da turjiya.
Kai ma sabon da ka zo jiya,
Ka ɗauka tamkar ka iya.
Makuna sha uku da kai kawai,
Babu kai, kai ka ce walƙiya.
Kai ko O'o na babba mai jaka,
Zan so ka ji zancan gaskiya.
Haƙƙimmu yana bisa kan wuya,
Naka kai ne kai yo ɗoriya.
Ka rantse har da Ubangiji,
Lafiyarmu da dukkan dukiya.
Ka tsare su ka alkinta su duk,
Zan so ka yiwo 'yar tariya.
In ka manta, shi fa Ubangiji,
Ba shi manta dare balle safiya.
'Yan ƙwaya sun cika lunguna,
Har saƙon dukkan nahiya.
'Yan siya ba sa taimako,
Sai wanda yake yin turjiya.
Koko loton kamfen in ya zo,
Sai ka gan su fa ɗauke da taliya.
Za su taka diro su yi cashiya,
Har alƙawari su yi ɗaukiya.
Sun manta dukkan alƙawar,
Allah na nan zai tambaya.
Wai shin mu sai yaushe ne
Za mu sanya idanun mikiya?
Mu yi dubi mui aiki da shi,
Don kare ƙasarmu guda ɗaya.
Don Allah yara da ƙanƙana,
Mu ƙyale batun sharholiya.
Ilimi mu riƙe shi da kyau ƙwarai,
Kar mu ce aiki yau yai wuya.
Mu riƙe su sana'a jumlatan,
Mu share batun sharholiya.
Ya Allah mu kam mun gaza,
Ka tsare mu da sharrin 'yan iya.
Ka ba mu rabo nan duniya,
Ka raba mu da faɗa Hawuya.
Mai waƙa wanda ake kira,
Mubarak ɗa na Bahaushiya.
Mubarak Idris Jikamshi ✍️
01/03/2026
Riga Ba Wuya
Tags
Ilimi