Cece-ku-ce ya kaure musamman yankin Arewacin Nijeriya tun bayan da aka fitar da sanarwar hauhawar farashin jarabawar Waec da NECO waɗanda ɗaliban Sakandire ke rubutawa domin tabbatar da sun kammala karatun su, daga ₦27,000 zuwa ₦50,000.
A daidai lokacin da al'umma ke fama da rashin tsarona kisa da satar mutane da kuma tsadar hauhawar farashin kayan masarufi, kwatsam sai kuma ga sabuwar sanarwar batun ƙarin kuɗin jarabawa na kimanin Naira duba ₦23,000 a kowace jarabawa guda. Lamarin da ya jefa al'umma cikin ruɗani da tambayoyi birjit a kan ƙarin da gwamnatin tarayya ta yi wa jarabawar, shin na mene ne?
Da yawan al'umma suna ganin matakin, an ɗauke shi ne, domin a hana 'ya'yan talakawa kammala karatun Sakandire ɗin ne, domin da ma tun farkon hawan mulkin Shugaban ƙasa Bila Ahmad Tinubu, ya janye tallafin man fetur da na karatu wanda hakan ya sabbaba tsadar kuɗin karatun gaba da Sakandire, tuni dubundubatar mutane suka ƙauracewa shiga bokon musamman karatun gaba da sakandire saboda rashin abin da za a biya kuɗin karatun da shi, sakamakon tsadar da ya yi. Kwatsam kuma sai ga wannan ƙarin shi ma ya biyo baya.
A irin zantawar da wannan rahoton ya yi da wasu mutane, sun bayyana cewa, "Ɗan aikin ɗan sanda da na sojan da 'ya'yammu ke samu ne ake yi ma baƙin ciki, shi ya sa ba a so su kammala karatun Sakandiren."
Jama'a da yawa na kuka da wannan ƙari, sai dai kuma wasu malamai na ji suna murna da wannan ƙarin da gwamnati ta yi, domin suna ganin wataƙila wannan zai sa iyaye su shiga taitayinsu su daina sakin 'ya'yansu sakaka ba su kula da karatunsu. Domin idan uba ya biya wa ɗansa ₦100,000 domin ya zana (rubuta) jarabawa, dole zai sanya ido a kansa don ganin ya yi ƙoƙari ya cinye jarabawar, ba kamar yadda suke yi idan an ba su kyauta ba.
A ɓangaren ɗaliban kuwa da na samu zantawa da wasu daga ciki, sun nuna takaicinsu da damuwa, tare da tunanin yanzu ina za su samu waɗannan kuɗaɗen su biya jarabawa? Da yawa abin da ɗaliban da na tattauna da su ke nan suke faɗa, musamman mara sa galihun cikinsu.