Farashin man fetur a Amurka ya sake tashi bayan makonni da dama yana sauka, sakamakon ƙarin tashin hankalin da ke tsakanin Amurka da Iran da kuma hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce matsakaicin farashin galan ɗaya na fetur ya ƙaru da cent shida a wannan mako, inda ya kai dala $3.88, wanda shi ne ƙaruwa mafi girma cikin mako guda tun tsakiyar watan Mayu.Hare-haren da aka kai kan wasu tankokin dakon mai a mashigar Hormuz da kuma musayar hare-hare tsakanin Amurka da Iran sun taimaka wajen haɓaka farashin ɗanyen mai na Brent da kusan kashi 5.5 cikin ɗari a wannan mako.
Rahotanni sun ce zirga-zirgar man fetur ta mashigar Hormuz har yanzu ba ta koma yadda take kafin rikicin ba.