A ranar Alhamis ne aka gabatar da Kofin Duniya na FIFA da za a ɗaga a New Jersey ranar Lahadi wanda yake ɗauke da zinari mai darajar kusan dala dubu ɗari bakwai da sha uku (713,000) wadda ta yi daidai da yuro ɗari biyar da talatin da biyu (£532,000) a cikinsa, har wa yau kofin yana da nauyin kilogram shida da ɗigo ɗaya da bakwai da biyar (6.175,) bisa wani doron bincike da London Stock Exchange Group (LSEG) suka gudanar.
Wani ɗan sassaƙa na Italiya mai suna Silvio Gazzaniga ɗan ƙasar Italiya shi ne ya sassaƙa shi kuma ya tsara shi, sannan aka sake ƙera shi a wurin aikin Bertoni da ke Milan ta Italiya. Ƙungiyar da za ta yi nasara a gasar da za a fafata a daren yau Lahadi tsakanin Argentina da Sifaniya za ta ɗaga kofin ne kawai na ɗan lokaci, sannan daga baya ta mayar da shi nan take domin a mayar da shi ma'ajiyarsa.
Ƙasar da za ta yi nasara za ta koma gida da wani kwafin kofin ne, wanda aka yi wa rufin zinariya, yayin da ainihin kofin zai koma rumbun adana kayayyaki na gidan tarihi da ke Zurich.