Rundunar tsaron SafeCity Security Service ta Jihar Delta, tare da hadin gwiwar jami'an rundunar 'yan sandan jihar, sun kama wani fitaccen dan bindiga da ake nema ruwa a jallo mai suna Abubakar Usman.
An kama shi ne bayan yin garkuwa da wata mata mai suna Blessing Chiedu, 'yar Masarautar Umunede, wadda aka sace a ranar 2 ga Yuli, 2026, a kan hanyar Ani-Ifekide Farm Road da ke Ubulu-Uku. Masu garkuwar sun bukaci iyalanta su biya kudin fansa na Naira miliyan 100.
Mai magana da yawun rundunar SafeCity Security Service, Harrison Gwamnishu, ne ya baiyana hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba.
A cewarsa, da zarar ya samu rahoton lamarin, sai ya sanar da hukumomin da abin ya shafa, inda rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ta rundunar 'yan sandan Jihar Delta da ke Asaba, karkashin jagorancin CSP Osakpolor, ta fara aiki.
Ya ce ta hanyar amfani da tsarin sa ido na Hydra Tech Surveillance System, jami'an tsaron suka kaddamar da aikin ceto cikin hadin gwiwa, inda suka samu nasarar kubutar da Blessing Chiedu da ranta ba tare da ta ji wani rauni ba a kan hanyar Ubulu-Unor/Ashama Road.
Bayan ceton ta, jami'an tsaron suka ci gaba da farautar masu garkuwar da suka tsere, har zuwa wayewar garin ranar Laraba, lokacin da tsarin sa ido ya gano maboyarsu a cikin dajin Ogwashi-Uku/Adonta da ke Jihar Delta.
Gwamnishu ya ce, "An yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da masu garkuwar, inda hadaddiyar tawagar jami'an ta yi nasarar rinjayar masu laifin. An kama daya daga cikin wadanda aka fi nema, Abubakar Usman, yayin da sauran mambobin kungiyar suka tsere zuwa cikin daji dauke da makamansu."
Ya kara da cewa bincike ya nuna cewa Abubakar Usman da kungiyarsa ne ke da alhakin aikata hare-haren garkuwa da mutane da dama a yankunan Igbodo, Umunede da sauran al'ummomin da ke makwabtaka, inda suka karbi miliyoyin nairori a matsayin kudin fansa daga iyalan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
