A shafinsa na Facebook mai suna Rt. Hon. Yahaya Abubakar Kusada, ya yi tsokaci gami da tambihi kan dambarwar da ake ta sa toka sa katsi a kanta, ta batun cin mutunci a siyasar Nijeriya. Ɗan Majalisar ya yi wa rubutunsa take da: "Pantami a Fagen Siyasa: Fuskantar Dokar Wasan Siyasa"
Inda ya kwafi wasu batutuwa daga cikin littafin Sheikh Abubakar Gini mai suna "Where I Stand" cewa: "Siyasa ba ta da wata kulawa ta musamman ga matsayin mutum ko darajarsa a cikin al’umma. Da zarar mutum ya shiga siyasa, hatta wanda ba shi da wani matsayi ko kima zai iya tsayawa ya zage shi ko ya yi masa magana ba tare da wata kunya ba."
Ɗan Majalisar ya ci gaba da sharhi kan dambarwar inda ya nuna yadda Al'umma suka yi Allah wadai da waƙar da Rarara ya yi a kan Pantami ta rashin girmamawa, inda ya ce: "Tun bayan da Rarara ya fitar da sabuwar wakarsa mai suka ga Malam Isa Ali Pantami, kafafen sada zumunta sun cika da ce-ce-ku-ce. Masu goyon bayan Malam Pantami da kuma dimbin Musulmi sun bayyana rashin jin dadinsu, suna ganin kalaman da Rarara ya yi sun wuce gona da iri kuma sun nuna rashin girmamawa ga wani malami da ake darajantawa."
Sai dai a nasa hasashen Hon. Ya ce: "Kafin mutum ya yanke hukunci kan wannan lamari, ya kamata ya fara fahimtar yanayin siyasar Nigeria da kuma matsayin Rarara a cikin wannan siyasa."
Hon. Ya bayyana fagen siyasa a matsayin wani dandali da ake saukalen rashin ɗa'a da rashin mutunci, ga dai abin da ya bayyana a rubutunsa: "Shekaru da dama, malamai da fastoci sun guji shiga siyasa saboda ana kallon siyasar Nigeria, har ma da ta Afirka gaba ɗaya, a matsayin fage mai cike da rashin ɗa’a da rashin mutunci. Saboda haka, da yawa daga cikin malamai sun fi zaɓar su tsaya gefe domin kare mutuncinsu da martabar addini. Wannan ya sa siyasa ta ci gaba da kasancewa a hannun waɗanda ake zargi da rashin nagarta da rashin kishin al’umma."
Shin waɗannan malami nasa, na nufin duka 'yan siyasa ba su da ɗa'a da mutunci ne ko kuwa ne yake nufi? Ko kuwa sai yana so ya ce da ma Rarara da iyayen gidansa ba su da ɗa'a ne?
A taƙaice Hon. Ya yi taƙaitaccen bayani a kan wane ne mawaƙi Rarara a siyasar Nijeriya inda ya bayyana cewa: "Rarara ɗan siyasa ne ta fuskar rawar da yake takawa. Wannan tsarin siyasa ne ya ba shi suna, ya sa ya zama sananne kuma ya kusanci masu iko a ƙasar nan. Ya taso ne a cikin siyasar da suka, zarge-zarge, da yaɗa farfaganda suka zama ruwan dare. Yanzu kuma, ga wani sabon ɗan siyasa wanda kuma babban malami ne da Musulmi da dama ke girmamawa—Malam Isa Ali Pantami. Rarara ya yi masa martani ne da irin salon siyasar da ya saba da shi, wato salon da ya daɗe yana gudana a siyasar Nigeria.
Matsayar Hon. Yahaya Abubakar Kusada a kan wannan batu ta ya tayar da zaune tsaye a jiya musamman a kafafen sada zumunta:
"A mahangar ɗabi’a da tarbiyya, ana iya cewa Rarara ya yi kuskure saboda kalamansa sun ɓata wa mutane da dama rai kuma sun nuna rashin girmamawa. Amma idan aka duba ta fuskar siyasa, musamman irin siyasar da aka saba da ita a Nigeria, abin da ya yi ba sabon abu ba ne. Tsarin siyasar da ya ba shi suna shi ne ya koyar da irin wannan salon. Wannan ba yana nufin abin da ya yi daidai ba ne. Sai dai yana nuna cewa muddin mutanen kirki da malamai suka ci gaba da nisantar siyasa, za ta ci gaba da kasancewa karkashin tasirin waɗanda suka ɗauki zagi, cin mutunci da farfaganda a matsayin dabarun siyasa."