Wani dan kasuwa dan Najeriya da ya dawo daga Birtaniya domin zuba jari a ƙasar, Charles Avwenagha, ya ce yana tunanin komawa Ingila na dindindin tare da yin watsi da fasfo din Najeriya bayan kasuwancin da ya kafa a Abuja ya lalace sakamakon rushewar da Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta yi masa.
Avwenagha ya bayyana cewa FCTA ta rushe kasuwancinsa mai suna Stopover Bar and Grill da ke Lokogoma a ranar Talata ba tare da ba shi wata sanarwa ta hukuma ba.
Ya ce, “Yayin da nake magana da ku yanzu, ina tunanin ƙirga asarata, in tattara kayana in koma Ingila, har ma in yaga fasfo din Najeriya. Ina da abokai a Birtaniya da suka yi hakan, kuma ni ma ina tunanin yin hakan.”
Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a wurin da aka rushe kasuwancinsa, wadda Per Second News ta wallafa a ranar Alhamis.
A cewarsa, abin da ya sa ya fara kwashe kayansa shi ne jita-jitar da ta yadu mako guda kafin rushewar cewa hukumomin FCT za su karɓe filin.
“Na ji jita-jita kusan mako guda da ya gabata cewa za su zo su karɓe wannan fili. Amma babu wanda ya ba ni wata sanarwa, babu wanda ya kawo min takardar gargadi,” in ji shi.
Ya ce ya rufe kasuwancin da kansa a ranar Lahadi sannan ya fara kwashe kayan aiki. Amma da safiyar Talata, yayin da ma’aikata ke cire wasu sassan ginin, kwatsam bulldoza suka iso.
“Da misalin karfe 12 zuwa 1 na rana, bulldoza suka zo. Sun ga mutane a saman rufi suna cire katako, masu walda suna aiki, amma suka umurce su su sauko sannan suka rushe komai har ƙasa,” in ji shi.
Avwenagha ya ce ya kafa kasuwancin ne shekara ɗaya da wata uku da suka gabata, kuma ya karɓi rancen fam 75,000 a Birtaniya domin ya zuba jari a Najeriya bayan an ƙarfafa masa gwiwar komawa gida.
Ya ce bai taɓa samun kwangilar gwamnati ba kuma bai san kowa a gwamnati ba.
“Na zo da kuɗi daga Birtaniya domin in zuba jari a nan. Yanzu ni ne zan biya wannan bashi. Ina da ma’aikata 84 da nake ciyarwa a wannan wuri. Abin yana da zafi. Na tsaya ina kallon yadda aka rushe komai. Babu wanda ya damu,” in ji shi.
Ya kuma tambayi ko har yanzu ya dace a ci gaba da ƙarfafa ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje su dawo su zuba jari a ƙasar, yana mai cewa mutane da dama sun rasa ayyukansu a yankin Lokogoma.
“Yanzu za ku ce in shawo kan wani daga kasashen waje ya zo ya zuba jari a Najeriya? Ku duba mutane 84 da suka rasa aiki. A wannan yanki kaɗai, ba tare da ƙari ba, aƙalla mutum 300 sun rasa ayyukansu. Shin haka ake samar da ayyukan yi?” in ji shi.
Ya ambaci wasu kasuwanni da ke kusa kamar Barbados, Amalashita, RM’s Gym, Hunter’s da Ari’s waɗanda ya ce su ma an rushe su.
Manajan Stopover Bar and Grill, Muktar Yahaya, ya tabbatar da labarin, yana mai cewa ma’aikata na ci gaba da kwashe kayansu lokacin da tawagar rushewar ta iso ta kore su daga wurin.
Sauran ma’aikatan, ciki har da Eze Chidimma, su ma sun bayyana cikin alhini yadda suka rasa ayyukansu ba zato ba tsammani.
Tawagar Per Second News ta kai ziyara wurin da abin ya faru a Lokogoma, inda aka nuna tarkacen ginin da aka rushe tare da bayanan dan kasuwar da ma’aikatansa.
A cikin ’yan watannin nan, hukumomin FCT sun gudanar da jerin rusau a sassa daban-daban na Abuja, inda suke cewa suna rushe gine-ginen da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a filayen gwamnati.
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sha kare matakin rusau, yana cewa ana yin hakan ne domin kare rayuka da dukiyoyi da kuma dawo da tsarin asalin ginin Abuja.
Ya kuma sha alwashin ci gaba da rusau duk da suka da korafe-korafen da mazauna yankin, ’yan majalisa da ƙungiyoyin fararen hula ke yi.
A watan Disambar 2024, Majalisar Dattawa ta buƙaci Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA) ta dakatar da ƙarin rusau, sai dai idan kotu mai hurumin shari’a ta bayar da umarni.
Sai dai Wike ya ce babu ja da baya, yana mai zargin waɗanda abin ya shafa da kwace filayen gwamnati tare da yin watsi da zarge-zargen da masu suka ke yi masa.