Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta rattaba hannu kan Yarjejeniya da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) domin fara koyar da digiri na biyu (MBA) a fannin gudanar da ayyukan Hajji.
Shugaban hukumar NAHCON Ambasada Ismail Abba Yusuf ya bayyana cewa wannan matakin wani bababn ci gaba ne da zai bunƙasa yadda ake gudanar da harkokin Hajji da Umrah a Najeriya.
"Gudanar da aikin Hajji na ƙara zama abu mai sarkakiya, hakan na buƙatar ƙwararrun ma'aikata masu ilimi, ƙwarewa da fahimtar yadda aikin Hajji ke sauyawa," in ji shugaban NAHCON Shugaban NAHCON Ambasada Ismail Abba Yusuf, da Sakataren Hukumar, Dakta Mustapha Muhammad Ali, ne suka sanya hannu a madadin NAHCON. Shugaban ABU, Farfesa Adamu Ahmed, tare da Magatakardar jami'ar, Malam Rabiu Samaila, su ma sun rattaba hannu kan yarjejeniyar.
Shugaban Jami'ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ya ce wannan shiri ya samo asali ne bayan shafe kusan shekara goma ana tattaunawa da haɗin gwiwa tsakanin jami'ar da NAHCON.
Za a gudanar da shirin digirin ta hanyar tsarin karatu daga gida.
Za kuma a buɗe shirin ga jami'an NAHCON, hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, kamfanonin Hajji da Umrah masu lasisi, masu aikin sufuri, yawon buɗe ido da otal-otal, malamai, 'yan kasuwa da kuma waɗanda suka kammala jami'a da ke son yin aiki a fannin gudanar da aikin Hajji a Najeriya da ma ƙasashen duniya.
"Wannan shi ne karon farko da irin wannan shiri zai taimaka wajen inganta ƙwarewa da ayyukan da ake yi wa alhazai, tare da mayar da Najeriya cibiyar ƙwarewa ta duniya a fannin ilimi," in ji NAHCON.