Michael Carrick ya yi magantu a kan Senne Lammens bayan dawowarsa Manchester United, sakamakon abin da ya faru da shi a Belgium a gasar cin kofin Duniya.
Ɗan Jarida: Michael, Senne Lammens ya dawo filin ɗaukar atisaye na Carrington bayan kammala gasar cin kofin Duniya da ta gabata a Amurka da Canada da kuma Mexico, Me kuka tattauna da shi a kan kuskuren da ya yi wa Belgium wanda ya kai ga an ci su ƙwallo wadda ta yi sanadiyyar dawowarsu gida. Me ka faɗa masa?
Michael Carrick: “Senne ya dawo yana ɗauke da abubuwa da yawa a cikin ransa, hatta jikkarsa cike yake da abubuwa masu yawa. Nan take na gane cewa har yanzu kuskuren da ya yi yana nan cikin tunaninsa. Na faɗa masa cewa, a matsayinka na mai tsaron raga, za ka iya yin kuskure ɗaya kawai, wanda duk duniya sai kowa ya tuna da shi, amma wannan ba ya bayyana aikinka gaba ɗaya.
“Na fada masa, ‘Senne, za ka yi kuskure a ƙwallo. Duk mai tsaron raga yakan yi. Abin da ya fi muhimmanci shi ne abin da za ka yi a karo na gaba da ka fita filin wasa." Gasar Cin Kofin Duniya ta ƙare. Don haka sai mu shirya wa gaba.
“Na tuna masa cewa Manchester United ba mu saye shi ba saboda muna tsammanin zai kasance cikakke. Mun saye shi ne saboda muna imani da ƙarfinsa, tunaninsa da kuma hazaƙarsa. Wani kuskure guda ɗaya ba zai goge komai na dalilin da ya sa muka sawo shi ya zo nan ba.
“Haka kuma na faɗa masa kada ya matsa wa kansa kan ƙoƙarin dole sai ya sauya a cikin atisaye guda ɗaya rak. Ya ɗauki lokacinsa, ya kwantar da hankalinsa ya dawo ya sanya sabon ɗanba na shiri ya kuma yi aiki tuƙuru. Mafi kyawun amsar da ɗan wasa zai iya bayarwa bayan kuskure ba tattaunawa ba ce ko neman gafara ba a’a, sai dai gyara abin da ya yi a filin wasan a baya.
“Senne matashi ne, mai hazaƙa kuma yana da ƙudirin gaske. Na san wannan kuskuren zai cutar da shi na ɗan lokaci, amma wani lokaci irin waɗannan lokutan suna sa ka ƙara ƙarfi. Aikina shi ne in tabbatar bai bar kuskure ɗaya ya zama labarin aikinsa ba. A Manchester United, za mu taimaka masa ya rubuta sauran labarin aikinsa.”