Sarki Sanusi Ya Goyi Bayan Sauye-sauyen Tattalin Arziki Da Tinubu Ke Yi

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya nuna goyon bayansa ga sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bullo da su, musamman matakan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke dauka wajen daidaita tattalin arzikin kasar.

Tinubu da Sarki Sanusi

Sanusi, wanda ya taba zama gwamnan CBN, ya ce matakan da aka dauka sun taimaka wajen fitar da Najeriya daga barazanar durkushewar tattalin arziki, tare da rage yawan kudaden da ke yawo da kuma daidaita darajar Naira.

Ya ce duk da cewa kudin ruwa na ci gaba da kasancewa mai yawa, an samu nasarar daidaita canjin Naira, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ke raguwa a hankali.

Sarkin ya kuma bayyana cewa ajiyar kudaden kasashen waje na Najeriya ya haura dala biliyan 40.

A cewarsa, tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba fiye da yawan karuwar al’umma, inda tattalin arzikin ya bunkasa da sama da kashi uku cikin dari a rubu’i na farko da kuma sama da kashi hudu a rubu’i na biyu.

Sanusi ya bayyana hakan a matsayin alamar samun sauki da kyakkyawan fata ga tattalin arzikin Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post