Dangote Zai Ba Da Kashi Daya Bisa Uku Na Dukiyarsa Ga Ayyukan Jin Kai – Halima Dangote

'Yar hamshaƙin attajirin Afirka, Aliko Dangote, wato Halima Dangote, ta bayyana cewa mahaifinta ya tsara ba da kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa ga ayyukan jin ƙai a matsayin wani ɓangare na tsarin gadonsa.

Dangote

Halima, wacce ke cikin amintattun gidauniyar Aliko Dangote Foundation, ta shaida wa Bloomberg cewa Dangote ya samu amincewar iyalansa kan wannan tsari domin tabbatar da cewa ayyukan agaji za su ci gaba har zuwa al'ummomi masu zuwa.

Ta ce Dangote ya riga ya tanadi tsarin da gidauniyar za ta fi mayar da hankali kan lafiya da ilimi, inda ya ware kaso mai yawa na dukiyarsa domin tallafa wa ayyukan jin ƙai.

A cewarta, an tsara wannan ne bisa tanadin shari'ar Musulunci da ke bai wa mutum damar ware kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa ta hanyar wasiyya domin ayyukan alheri.

Halima ta ƙara da cewa ba da gudummawa ga al'umma wani muhimmin ɓangare ne na manufofin iyalansu, kuma suna ganin nasarar kasuwancinsu na da alaƙa da taimakon jama'a.

Gidauniyar Aliko Dangote, wacce aka kafa a shekarar 1994, tana gudanar da ayyuka a fannonin lafiya, ilimi, abinci mai gina jiki da agajin jin ƙai, inda mafi yawan ayyukanta ke gudana a Najeriya, sannan tana tallafa wa wasu ƙasashen Afirka.

A farkon shekarar nan, mujallar TIME ta sanya Aliko Dangote cikin jerin fitattun masu ayyukan jin ƙai na duniya, tare da bayyana cewa gidauniyarsa na kashe sama da Naira biliyan 50 a duk shekara wajen gudanar da ayyukan agaji a nahiyar Afirka.

Post a Comment

Previous Post Next Post