Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta ceto fasinjoji 10 bayan harin da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai kan wata motar haya a kan babbar hanyar Jos zuwa Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Haruna, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce 'yan bindiga biyar dauke da adduna da bindiga guda sun tare hanya, inda suka kai hari kan motar kasuwanci kirar Toyota Hiace mai lambar rajista BKK 6824 XA, wadda ke kan hanyarta daga Jos zuwa Kano. Maharan sun yi awon gaba da fasinjoji 13 cikin mutum 20 da ke cikin motar.
Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Yuli, 2026, da misalin karfe 5:30 na yamma, a yankin Dajin Falgore da ke Karamar Hukumar Doguwa, tsakanin Gate Two Safer Highway da Dogo Dutse.
Da samun kiran gaggawa, Jami'in 'Yan Sanda mai kula da Sashen Doguwa (DPO) ya tura jami'an rundunar na musamman zuwa wurin, inda suka fafata da maharan a musayar wuta.
Sakamakon wannan gaggawar daukar mataki, an samu nasarar ceto mutane tara nan take, yayin da wani namiji ya tsere daga hannun masu garkuwar daga baya, lamarin da ya kai adadin wadanda aka ceto zuwa mutum 10.
Sai dai har yanzu mutane uku na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwar, wadanda suka hada da namiji daya da mata biyu.
Rundunar ta ce an garzaya da wadanda aka ceto zuwa Babban Asibitin Doguwa domin duba lafiyarsu, kuma suna samun kulawa tare da kasancewa cikin kwanciyar hankali.
Sanarwar ta kara da cewa an kara tura jami'an tsaro na musamman tare da karfafa aikin tattara bayanan sirri domin ceto sauran mutanen da ke hannun masu garkuwar tare da cafke wadanda suka tsere.
Rundunar ta bayyana cewa wannan nasarar ta nuna kudurin Rundunar 'Yan Sandan Najeriya karkashin jagorancin Sufeto Janar na 'Yan Sanda na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta hanyar daukar matakin gaggawa da hadin gwiwa da al'umma.
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya yaba wa mazauna yankin da masu amfani da hanyar saboda bayar da sahihan bayanai cikin gaggawa, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'umma a fadin jihar.
Ya kuma ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma za a sanar da jama'a duk wani sabon ci gaba da aka samu.